Liverpool ta ƙi yadda da tayin ɗaukar Gordon daga Newcastle

Anthony Gordon

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Liverpool ta ƙi yadda da tayin ɗaukar Anthony Gordon, ita kuma ta bayar da Jarell Quansah zuwa Newcastle United.

Ƙungiyar Anfield ta kalli musayar ba riba a wajenta, duk da cewar ɗan wasa Gordon mai shekara 23 ƙwararre ne kuma irin wanda take son ɗauka ne.

Gordon, wanda ya koma Newcastle United kan £45m a Janairun 2023, yana tare da tawagar Ingila da take buga 2024 a Jamus.

An kuma saka shi wasa ranar Talata a karawar da Ingila ta tashi 0-0 da Slovenia ranar Talata, kuma karawar da yayi kenan kawo yanzu.

Ɗan wasan da Paris St-Germain ke son yin zawarci, ya ci ƙwallo 11 a lik a Newcastle, kuma shi ne ya lashe ƙyautar fitatcen ɗan wasa a ƙungiyar a 2023/24.

Liverpool ba ta taya ɗan ƙwallon Newcastle ba, sannan ba ta da niyyar rabuwa da matashinta mai shekara 21 Quansah.

Mai tsaron bayan ya fara buga wa Liverpool wasanni tun daga bara, yana cikin 'yan wasan Ingila na ƙwarya-ƙwarya zuwa Euro 2024 daga baya aka bayyana 26 da ba shi a ciki.

Haka kuma Liverpool tana da ƴan wasan da ke buga gaba da yawa da suka hada da Mohamed Salah da Darwin Nunez da Luis Diaz da Cody Gakpo da kuma Diogo Jota.

BBC ta tuntuɓi Newcastle don jin karin bayani kan lamarin.