Waiwaye: 'Yan bindiga 'sun yaudari' gwamnatin Najeriya, wasu sun sace amarya da ango a Jihar Katsina
A wannan maƙala, mun yi waiwaye kan muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya a wannan makon da muke bankwana da shi.
'Yan bindiga sun yi garkuwa da Amarya da Ango a birnin Katsina

Asalin hoton, Other
'Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu sabbin ma'aurata bayan kashe jami'an sa-kai biyu a wani hari da suka kai unguwar Shola da ke birnin Katsina.
A cewar mazauna unguwar 'yan bindigar sun far mu su ne da misalin ɗaya da minti ashirin da biyar na dare, kuma sun shafe sa'a guda su na harbe-harbe.
Sun shaida cewa 'yan sa-kai sun rasa rayukansu ne a kokarin hana garkuwa da ma'auranta, sannan an jikkata wasu daga cikinsu.
Rahotanni na cewa dole ta sanya masu aikin sa-kai janye jiki bayan sun fahimci cewa 'yan bindigar sun fi karfinsu.
Wani mazaunin unguwar ta Shola da ke cikin Katsina ya shaida wa BBC cewa ‘yan bindigar sun shiga unguwar ne bisa babura jiya dauke da bindigogi suna harbe-harbe.
Mutumin yace ‘yan bindigar sun fasa wani gida ta baya suka shiga. Al’amarin dai yayi sanadin mutuwar mutum biyu sanann mutum biyu suka jikkata.
Ya kuma ce baya ga ma'auratan akwai mutane da dama da aka sace, sai dai bai san adadi ba.
Wannan dai ba shi ne karon farko da mahara ke aukawa unguwar Shola ba, ko fiye da wata guda ma ‘yan bindiga sun shiga yankin.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina SP Gambo Isah ya tabbatar da aukuwar wannan hari, inda ya ce jami’ansu sun dukufa don kuɓutar da amarya da angon.
Bugu-da-kari SP Gambo ya ce sun kubutar da wasu mutum shida da aka yi garkuwa da su a kauyen Tandama cikin karmar hukumar Danja, bayan wani samame da suka kai maboyar ‘yan bidiga.
Haka kuma, ya ce a yankin karamar hukumar Safana ma, sun yi nasarar kashe wani kasurgumin dan fashin daji Albdulkarim Faca-Faca da mutanansa bakwai a karshen mako, bayan barin wutar da wani jirgin yaki ya yi akan maboyarsu.
Buhari ya gana da 'yan uwan fasinjojin jirgin kasa na Abuja-Kaduna bayan wata biyar da sace su

Asalin hoton, State House
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da wasu daga cikin fasinjojin jirgin kasan da 'yan bindiga suka sace daga Abuja zuwa Kaduna a watan Maris.
Shugaban kasar ya gana da mutanen ne ranar Alhamis a fadar Aso Villa da ke Abuja kwana daya bayan sako karin mutum biyar da aka sace a jirgin kasan.
Wannan ne karon farko da mutanen ke ganin Shugaba Buhari tun bayan yin garkuwa da 'yan uwan nasu a watan Maris na 2022.
Ganawar tasu na faruwa ne makonni kadan bayan 'yan bindigar sun sha alwashin sace shi kansa shugaban kasar da kuma gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai.
Sun yi barazanar sace shugaban kasar ne a wani bidiyo da suka fitar wanda ya nuna su suna lakada wa fasinjojin duka.
Har yanzu dai akwai sauran fasinjojin da ke hannun 'yan bindigar, wadanda suka yi barazanar kashe su idan gwamnati ba ta biya musu bukatunsu ba.
Shugaba Buhari ya sha kakkausar suka daga wurin 'yan kasar bisa abin da suka kira rashin kubutar da fasonjojin duk kuwa da umarnin da ya bai wa jami'an tsaro na yin hakan.
A ranar 28 ga watan Maris ɗin 2022 ne masu tayar da ƙayar baya suka kai wa jirgin ƙasan da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna hari da daddare.
'Barayin fasinjan jirgin kasa sun yaudari gwamnati bayan sakin iyalansu'

Asalin hoton, Other
Fadar Gwamnatin Najeriya ta ce 'yan bindigar da suka yi garkwua da fasinjnojin jirgin ƙasa na Abuja zuwa Kaduna sun yaudare ta bayan ta biya musu wasu buƙatu yayin tattaunawar da suke yi da zimmar sako fasinjojin.
Bayanan na fitowa ne 'yan awanni bayan Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis ya gana da 'yan uwan fasinjojin fiye da 60 da aka sace a watan Maris na 2022.
Mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa, Garba Shehu, ya faɗa wa BBC Hausa cewa gwamnati ta biya wa shugaban 'yan bindigar buƙatarsa da ya nemi a saki matarsa mai ciki, "amma sai suka sake bijiro da wasu buƙatun".
Ba wannan ne karon farko da aka ji cewa 'yan bindigar sun saɓa alƙawarin da aka yi da su ba a tattaunawar, amma shi ne karon farko da gwamnatin ta faɗa da bakinta da kuma ainahin buƙatun masu garkuwar.
"Shugaban 'yan ta'addan nan ya buƙaci a saki matarsa mai ciki. Gwamnati ta kai ta asibiti kuma ta haifi tagwaye, aka nuna masa cewa matarsa da 'ya'yansa na cikin ƙoshin lafiya, kuma aka miƙa wa iyayensa su," in ji Garba Shehu.
Yayin ganawar, Buhari ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta yi amfani da ƙarfi ba wajen ceto 'yan uwan nasu, yana mai cewa "abin da na saka a gaba shi ne a sake su da ransu".
Har yanzu akwai mutum aƙalla 31 da masu garkuwar ke riƙe da su a cikin daji, a cewar gwamantin, wadda ta ce ba za ta yi amfani da ƙrfi ba wajen ceto su.
Joshua Dariye na shan suka kan yunƙurin tsayawa takara bayan yafe masa laifin satar kuɗi

Asalin hoton, EFCC
Masu yaki da rashawa a Najeriya na sukar wani yunkuri da aka ce tsohon gwamnan jihar Filato, Joshua Dariye ke yi na sauya-sheka zuwa Jam`iyyar Labour da nufin neman takarar kujerar sanata ta mazabar Filato ta tsakiya.
Wasu dai na ganin cewa bai kamata mutumin da kotu ta kama da laifin badakala na makudan kudade ya sake neman shugabancin al`umma ba.
A ranar Litinin ne aka saki tsohon gwamnan da wasu daga gidan yari, bayan ya shafe kusan shekara hudu a daure, sakamakon kama shi da laifin wawure kudin gwamnatin jihar fiye da naira miliyan dubu daya.
Kasa da mako guda da sakin tsohon gwamnan, maganar sake tsayawa takararsa domin neman kujerar Sanata a mazabar Filato ta tsakiya ta fara fitowa kuma a hankali maganar sai kara karfi take yi.
Wasu rahotanni na cewa an kammala shirin karbar sa a jam`iyyar Labour tare da share masa hanyar shiga takara.
Sai dai masu yaki da rashawa a Najeriyar na cewa bai kamata a ba shi wannan damar ba, ganin cewa dawowarsa ke nan daga gidan yari, sakamakon daurin da aka yi masa, bayan kotu ta kama shi da laifin cinye kudin jihar ta Filato a zamanin da yake gwamna.
Auwal Musa Rafsanjani shi ne wakilin kungiyar Transparency International a Najeriya kuma ya bayyana cewa wannan ya nuna cewa yaƙi da cin hanci da rashawa da ake yi a Najeriya ya zama wasan yara.
"Idan Buhari ya ce ya yafe, ai jama'ar da aka sace kuɗinsu waɗanda suna nan suna fama cikin wahala da yunwa da talauci ai su ba su yafe ba," in ji Rafsanjani.
Najeriya ta bankaɗo kudi sama da naira biliyan uku da aka sace daga ƙasashen waje
Gwamnatin tarayya ta banƙaɗo sama da N3.2bn na kuɗaɗen da aka sace a shari'ance daga watan Maris na 2021 zuwa Mayu na 2022.
Wannan na zuwa ne saboda an samu naira biliyan N1.82 daga sayar da fom din gwanjo da ma sayar da kadarori a shekara 18 na farko a mulkin Buhari.
Ministan Shari'a Abubakar Malami ne ya bayyana hakan ga 'yan jarida ranar Alhamis a zama na 46 da aka yi a fadar shugaban ƙasa wanda kwamitin sadarwar shugaban kasa ya shirya.
Malami ya bayyana cewa an riga an yi amfani da kudaden da aka gano a kan ayyukan sun ƙunshi gadar Niger ta biyu, titin Kano zuwa Abuja da babban titin Lagos zuwa Ibadan.
Shugaban Ghana ya ƙaryata nuna goyon baya ga Peter Obi

Asalin hoton, AFP
Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo ya musanta nuna goyon bayan ɗan siyasar Najeriya kuma dan takarar shugaban ƙasa Peter Obi, biyo bayan yaɗa jita-jitar faruwar haka akan shafukan zumunta na kasashen biyu da ke yammacin Afirka.
Shugaba Akufo-Addo ya ce wannan batu "karya ce kuma neman rigima ne".
Ghana da Najeriya sun shafe gomman shekaru da kyakkyawar dangantakar mai karfi tsakanins su, sun zama kamar ƴan uwa.
"Kuma ba zan zama wanda zai tsoma baki a kan lamuran cikin gida na siyasar Najeriya ba," ya ce a shafin Twitter.
Peter Obi na takarar shugabancin kasa a ƙarƙashin jam'iyyar ƙwadago ta Labour.
Najeriya za ta zabi sabon shugaban a watan Fabrairun 2023.









