Gane Mini Hanya - Yanayin tsaro a Arewa Maso Gabashin Najeriya
A kwanakin baya ne Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya shaida wa duniya cewa kimanin mayakan Boko Haram dubu dari ne suka ajiye makamai kuma suka mika wuya ga rundunar da ke wanzar da zaman lafiya a yankin ta Operation Hadin Kai.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 77. Da ma dai rundunar Operation Hadin Kai ta sha ikrarin samun irin wannan nasara. Rundunar ta ce ta riga ta karya lagon ‘ya’yan kungiyar ta Boko Haram.
Mustapha Musa Kaita ya tattauna da Manjo Janar Christopher Gwabi Musa, wanda shi ne babban kwamandan Rundunar Operation Hadin Kai da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Arewa maso gabashin Najeriya, kuma kwamandan ya fara da bayyana dalilin da ya sa aka kafa rundunar ta Operation Hadin Kai.







