Za a zuba jari a fasahar zamani don kaucewa hayaki mai gurbata muhalli

Asalin hoton, Getty Images
Cikin wani sabon rahoto kwararru a bangaren sauyin yanayi sun ce akwai bukatar amfani da hanyoyin fasahar zamani wajen kawar da hayaki mai gurbata muhalli a duniya.
Masana kimiyya sun ce rage hayaki mai gurbata muhalli ba zai wadatar wajen rage dumamar yanayi ba, dole sai an hada da wasu dabaru na fasahar zamani.
Yanayin da ake ciki a yanzu ba zai iya cire hayakin daga iskar da ake shaka ba.
Hayaki mai gurbata muhalli shi ne abin da ke dumama yanayi.
Sinadarin C02 shi ne sinadarin da ya fi ɗumama duniya, kuma ana fitar da shi ne idan makamashi kamar fetur ko gas na ƙonewa.
"Domin ƙayyade ɗumamar zuwa ƙasa da maki biyu a ma'aunin celcius, akwai buƙatar mu ƙara rage fitar da sinadarin." In ji Dr Steve Smith na jami'ar Oxford.
Ya ce," Duk wasu sabbin hanyoyi an yi amfani da su.".Akwai bayanan da masana kimiyya ke yi cewa duniya na dumama saboda irin sinadaran da ake fitarwa wadanda ke gurbata muhalli."
Sun ce idan har ba a dai-daita fitar da hayakin da ke gurbata muhalli da yanayi da kuma hanyoyin da za a rage shi ba, to za a ci gaba da fuskantar karuwar dumamar yanayi a duniya.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
To amma kai wa ga hakan shi ne babban aiki.
Rahoton Majalisar Dinkin Duniya na baya bayannan a kan sauyin yanayi ya ce idan har ana so a kawar da hayaki mai gurbata muhalli kwata kwata a duniya, to dole a rage sinadarin CO2, sannan a biya masana'antun da ke fitar da irin wannan sinadari diyya.
A yanzu tsirrai kamar bishiyoyi da makamantansu na taimakawa wajen cire sinadarin CO2.
Masana sun ce idan har ana so a rage fitar da wannan sinadari saboda gurbata muhalli to dole sai an rubanya a kan abubuwan da ake da ke rage fitar da sinadarin kafin na da 2050.
Hanyoyin fasahar da za a iya amfani da su wajen rage hayaki mai gurbata muhalli
Wani sabon rahoto mai taken " Yadda za a cire hayakin da ke gurbata muhalli" ya ce idan har ana so a rage dumamar yanayi akwai bukatar a zuna jari a harkokin fasahar zamani.
Hanyoyin da ake ganin za su taimaka na da yawan gaske, domin sai an hada da wadanda ake amfani da su da kuma wasu sabbi idan har ana so a kawar da dumamar yanayi.
Sauran hanyoyin kuma sun hadar da amfani da abubuwan da za su kawar da hayakin na suka jibanci fasahar zamani.

Asalin hoton, Getty Images
Akwai fargabar da ake cewa amfani da hanyoyin fasahar zamani wajen rage hayaki mai gurbata muhalli da kuma dumamar yanayi zai bukaci kashe mai yawa, sannan kuma za a iya amfani da hakan wajen jan kafa a kokarin da ake na kawar da dumamar yanayi a duniya.









