Mutanen da suka ceci ran juna duk da ba su taɓa haɗuwa ba

Asalin hoton, AFP
- Marubuci, Sharon Barbour and Natalie Wright
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- An wallafa
Sakamakon ba da gudummawar ƙwayoyin halitta ba tare da bayyana sunansa ba, Marius Werner ya ceci rayuwar wani likita ɗan Burtaniya - kuma, matashin Bajamushen ya ce, wataƙila hakan ma ya cece rayuwarsa, domin yin hakan ya ba shi manufa a rayuwa a lokacin da ya ke tunanin kashe kansa.
Yayin da ya ke fama da cutar kansa ta jini da ba kasafai ake samun ta ba, fatan Dr Nick Embleton kawai shine a yi masa dashen ɓargon ƙashi.
Kuma da aka kasa samun wanda zi iya ba shi a Burtaniya, sai aka baza bincike a faɗin duniya.
Shekara biyu bayan haka, BBC da ƙungiyar bayar da agaji ta Anthony Nolan sun taimaka wa "'yan'uwan na jini" wurin ganawa da juna a karon farko.
'Zai iya mutuwa'
Nick ya shafe fiye da shekara ashirin ya na aiki a sashen kula da jarirai na Newcastle, yana taimakawa wajen ceton dubban ƙananan yara marasa lafiya a duniya.
Amma a 2021, sai shi ma ya buƙaci kulawar likita.
Yana tafiya a cikin asibitin, ya ce "bai san abin da ke tafe ba".
"Na san cewa zan iya mutuwa, don haka na yi wasiyya," in ji shi.
“Na tattauna wannan batun da matata da yarana.
"Na yi bakin ciki saboda yarana - ba na son su girma tsawon rayuwarsu ba tare da mahaifinsu ba."

Dashen na sauya ƙwayoyin jinin da suka lalace da masu lafiya - amma jiki ya kan ƙi su kai tsaye sai dai idan an sami waɗanda suka dace.
Charlotte Hughes, daga ƙungiyar ba da agaji ta Anthony Nolan, ta ce: "Mun fara bincika rajistar Burtaniya kuma muna fatan samun wanda ya dace a nan.
"Idan ba mu iya samu ba, to Anthony Nolan zai bincika a duk duniya don nemo wanda zai dace.
"Ana iya samun dace daga ko'ina."
'Lamari cike da matuƙar damuwa'
Da mai bayarwa da mai jinyar dole ne su kasance ba a san sunansu ba har sai an san cewa an yi nasarn dashen.
Da ya fahimci hakan, bayan shekara biyu, Nick ya shaida wa BBC cewa yana son gano wanda ya ba shi gudummawar.
BBC tare da haɗin gwiwar Anthony Nolan, ta gano Marius, mai shekaru 24, daga Chemniz, kusa da birnin Dresden, wanda ke cikin rajistar masu ba da gudummawa tun yana matashi.
Kuma ya amince ya tashi zuwa Birtaniya ya gana da Nick, a cibiyar tallafawa masu fama da cutar kansa ta Maggie a Newcastle, a asibitin Freeman, inda aka yi aikin dashen.
Yayin da mutanen biyu suka rungume, Marius ya ce: "Na yi matukar damuwa – ina karkarwa."
'Babu damuwa'
Nick ya faɗa masa: “Kwayoyin cutar kansar duk sun watse.
“Lokacin da suka duba jinina, duk waɗannan ƙwayoyin jinin na ka ne.
“Ba don kai ba da na mutu
"Ina da yara huɗu – da sun rasa mahaifinsu.
"Abin da na ke son in ce shi ne, 'Na gode."
Ya rasa abin faɗa, Marius ya yi ƙokarin cewa: "Ba damuwa."
Yayin da hawaye ke kwarara a fuskokinsu, Nick ya raɗa masa: "Na gode sosai."
'Hawaye sun kwarara'
Daga baya, Marius ya tuna lokacin da ya gano cewa dashen ya yi aiki - kuma majinyacin ya tsira.
"Bayan wannan bayanin, hawaye ne kawai ke kwararo mun," in ji shi.
"Ina kan hanyar zuwa aiki sai da na tsayarda da motata na fito na shaki iskar waje - hawaye na ta zubowa."
Bayan haka, Marius ya bayyana cewa a baya ya yi ƙoƙari ya kashe kansa da kuma yadda - ta wata hanya - Nick ya taimaka ya cece shi.
"Na yi fama dukan rayuwata tun ina ɗan shekara 13 da matsalolin lafiyar ƙwaƙwalwa," in ji shi.
"Na sha wahalar samun gano ainihin manufar rayuwata.
"[Yanzu,] Zan iya cewa, 'Na yi wani abun da ya dace"
Kuma yayin da jini iri ɗaya ke bi ta jijiyoyinsu, yanzu mutanen biyu suna shirin ci gaba da zumunci da juna a matsayin “yan’uwan jini”.










