Waiwaye: Dokar taƙaita shekarun shiga jami'a da sukar Tinubu kan sayen jirgi

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Wannan maƙale ce da ke kawo muku muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi

Babban Sufeton 'yansandan Najeriya

Asalin hoton, NG POLICE

Babban Sufeton 'Yansandan Najeriya Kayode Adeolu Egbetokun ya ce waɗanda suka kashe dakarun rundunar biyu yayin tattakin mabiya mazahabar Shi'a a Abuja ranar Lahadi "sun kashe zaman lafiya".

Mai magana da yawun rundunar ‘yansandan Najeriya a Abuja, SP Josephine Adeh, ta ce jami'anta na tsaka da aikinsu a wani wurin bincike da ke kusa da Kasuwar Wuse ‘yan ƙungiyar ta IMN suka far musu.

A sanarwar ta ƙara da cewa sun kama mutum 97 da ake zargi da hannu a kisan.

Sai dai IMN ta musanta zargin, tana mai cewa mambobinta ba su kashe kowa ba yayin tattakin nasu na ranar Arba'in.

'Daga 2025 duk yaron da bai kai 18 ba ba zai shiga jami'a ba a Najeriya'

Ministan Ilimi na Najeriya

Ministan ilimin Najeriya, Farfeasa Tahir Mamman ya ce babu yaron da za a sake bari ya yi jarrabawar kammala sakandire ba tare da ya cika shekara 18 da haihuwa ba.

Farfesan wanda ya bayyana hakan yayin wata hira a shirin "Sunday Politics" ranar Lahadi na gidan talabijin na Channels, ya kara da cewa gwamnatin tarayya ta umarci hukumomin da ke kula da jarrabawar kammala sakandare ta WAEC da WASSCE da NECO da su bi sabon umarnin nata.

Ministan ya kuma ce sabuwar ƙa'idar ta shafi yaran da ke son yin jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandare - UTME da hukumar JAMB ke gudanarwa.

Ambaliya ta kashe mutum 185, ta raba fiye da dubu 41 da muhallansu a Najeriya

Ambaliya

Aƙalla mutum 185 ne suka mutu, sannan dubbai suka rabu da muhallansu bayan mamakon ruwan sama da ya jawo ambaliya a Arewacin Najeriya, kamar yadda Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta ƙasar, NEMA ta sanar a ranar Litinin

Jihohin Arewa uku da suka fi fuskantar ambaliyar su ne Jigawa da Adamawa da Taraba, kamar yadda Kakakin hukumar, Manzo Ezekiel ya shaida wa BBC.

Haka kuma ambaliyar ta lalata kusan hekta 694 na gonaki in ji shi.

NCC ta saka wa'adi na ƙarshe kan haɗa layukan waya da lambar NIN

Katin waya da katin dankasa

Asalin hoton, OTHERS

Hukumar sadarwa ta ƙasa a Najeriya ta ce ta bai wa kamfanonin sadarwa umarnin kammala haɗa lambobin waya da lambar ɗan ƙasa ta NIN zuwa ranar 14 ga watan Satumban 2024.

Nigerian Communications Commission (NCC) ta ce daga ranar 15 ga watan Satumba babu layin waya da za a sake sayarwa ba tare da haɗa shi da NIN ba.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar a yau Laraba ta ce zuwa yanzu, an haɗa layin waya sama da miliyan 153 da NIN - wanda ya nuna kashi 96 kenan cikin 100 na layuka a ƙasar.

Gwamnatin Najeriya ta ce ba za ta biya likitocin da ke yajin aiki albashi ba

Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Asalin hoton, STATE HOUSE

Gwamnatin Najeriya ta ce ba za ta biya likitocin da suka shiga yajin aiki na gargaɗi na kwana bakwai ba a asibitocin hukuma, albashi tsawon kwanakin da suka ƙaurace wa aikin.

Likitocin sun shiga yajin aikin na barazana ne, inda suke buƙatar a sako abokiyar aikinsu, Dr Ganiyat Popoola, wadda masu satar mutane suka sace wata takwas da ya wuce.

A wata sanarwa da ma'aikatar lafiya ta fitar ranar Alhamis, ta nuna matuƙar damuwa a kan matakin likitocin masu neman ƙwarewa (NARD), na shiga yajin aikin, duk da abin da ta ce ƙoƙarin gwamnati na ganin an sako likitar lami lafiya.

NNPCL zai mayar da matatun mai na Warri da Kaduna hannun 'yan kasuwa

Matatar mai

Asalin hoton, Getty Images

Babban kamfain mai na Najeriya NNPCL ya bayyana aniyarsa ta mayar da matatun man fetur na ƙasar da ke Warri da ta Kaduna hannun 'yan kasuwa.

Cikin wata sanarwa da kamfanin ya wallafa a shafin X, ya ce ya ɗauki matakin ne domin ci gaba da gudanarwa tare da kula da matatun biyu.

An kafa matatar Warri - wadda ke jihar Delta a yankin kudu maso kudancin ƙasar - a shekarar 1978, kuma tana da ƙarfin tace gangar mai 125,000 a kowace rana, bayan wasu albarkatun na fetur.

Ita kuwa ta Kaduna an ƙaddamar da ita ne a 1980, domin samar da man fetur ga yankin arewacin Najeriya, inda take iya tace ganga 110,000 a kowace rana.

Tsohon gwamnan Cross River ya soki Tinubu kan sayen sabon jirgin sama

Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Asalin hoton, PRESIDENCY

Tsohon gwamnan jihar Cross River, da ke kudu maso kudancin Najeriya, Donald Duke, ya soki Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan sayen sabon jirgin sama, a lokacin da 'yan kasar ke fama da yunwa, da cewa alama ce ta gazawar gwamnati.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Mista Duke, wanda ya kasance gwamnan jihar ta Cros River a tsakanin shekarun 1999 da 2007, ya faɗi hakan ne a lokacin hira da tashar talabijin ta Channels a ranar Juma'a.

Ya ce: ''Babu wata birgewa ka ce mutanenka na fama da matsalar rayuwa; gazawar shugabancinka ne. Idan ni ne shugaba a gida, zan so a ce iyalina suna da komai, ba zan so a ce suna cikin matsin rayuwa ba.''

A makon da ya wuce ne babban mai taimaka wa shugaban ƙasar kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya sanar da cewa gwamnatin ta sayo sabon jirgin saman.

A kan matsalar tsaro da ƙasar ke fama da ita Mista Duke, ya ce kamata ya yi shugaban ya tuhumi shugabannin hukumomin tsaron da ya naɗa.