Everton na son aron Grealish, Isak ya kusan zama mallakin Liverpool

Asalin hoton, Getty Images
Everton na son karɓo aron ɗanwasan gaba na Ingila Jack Grealish, mai shekara 29 amma tana fuskantar hamayya daga West Ham da Napoli. (ipaper - subscription required)
Alexander Isak, mai shekara 25, ya amince da buƙatun Liverpool kan yarjejeniyar shekara biyar idan har Newcastle ta amince da tayin ɗanwasan na Sweden. (Sky Sports Switzerland - in French)
Brentford ba ta shirya sayar da ɗanwasan gaba na DR Congo ba Yoane Wissa, mai shekara 28 ga Newcastle har sai ta samu madadinsa. (ipaper - subscription required)
Manchester United ta shiga hamayya kan ɗanwasan gaba na RB Leipzig da Slovenia Benjamin Sesko, mai shekara 22, wanda kuma ke tattaunawa da Newcastle. (Sun)
Chelsea na dab da cimma yarjejeniyar sama da sama da fam miliyan 34 domin ɗauko ɗanwasan baya na Netherlands Jorrel Hato daga Ajax. (Athletic - subscription required)
Manchester United ta taya ɗanwasan tsakiya na Sporting Morten Hjulmand, mai shekara 26, amma ƙungiyar na son a biya ta sama da fam miliyan 43 kan ɗanwasan na Denmark international, wanda kuma Juventus ke farauta (Calciomercato - in Italian)
Nottingham Forest na sa ido kan ɗanwasan gaba na Fulham da Spain Adama Traore, mai shekara 29, wanda ya taba taka leda ƙarƙashin Nuno Espirito Santo a Wolves. (Telegraph - subscription required)
Forest na dab da ɗauko aron ɗanwasan Switzerland Dan Ndoye, mai shekara 24, bayan ya sanar da Bologna yana son taka leda a gasar Premier ta Ingila. (Telegraph – subscription required)
Idan har Forest ta sha gaban Napoli kan Ndoye, ƙungiyar za ta mayar da hankali kan ɗanwasan gaba na Manchester City Grealish ko kuma ɗanwasan Manchester United da Argentina Alejandro Garnacho. (Sun)
Chelsea ba ta da niyyar rabuwa da ɗanwasan bayanta na Spain Marc Cucurella, mai shekara 27, duk da rahotannin da ke alaƙanta shi da ƙungiyoyin Saudiyya. (Football London)
Bayern Munich ce kawai ta nuna tana buƙatar ɗanwasan tsakiya na RB Leipzig Xavi Simons, mai shekara 22, amma ɗanwasan na Netherlands ya fi son ya koma taka leda a gasar Premier League. (Bild - in German)
Everton da West Ham da Nottingham Forest na hamayya kan ɗanwasan tsakiya na Brazil Douglas Luiz, mai shekara 27, wanda ke son barin Juventus a wannan bazara. (Gazzetta dello Sport - in Italian)
Manchester United a shirye take ta bayar da aron ɗanwasan tsakiya na Ingila Toby Collyer, mai shekara 21. (Daily Mail)











