Labaran wasannin BBC Hausa kai-tsaye daga 26/07 zuwa 01/08/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Asabar 26 ga watan Yuli zuwa 1 ga watan Agusta 2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Abdu, Umar Mika'il

  1. Liverpool na shirin haƙura da sayen Isak

    Isak

    Asalin hoton, PA Media

    Liverpool na shirin ficewa daga cinikin ɗanwasan gaba na Newcastle Alexander Isak bayan an ƙi karɓar tayin farko da ta bayar.

    Newcastle ta yi wa ɗanƙwallon farashi kan fan miliyan 150, inda ta ƙi amincewa da tayin 110 daga Liverpool kan ɗan ƙasar Sweden ɗin.

    BBC Sport ta fahimci cewa Liverpool ba ta tunanin cinikin zai faɗa a wannan bazarar saboda yadda al'amura suke a yanzu.

    Ɗanwasan mai shekara 25 bai shiga tawagar Newcastle da ta je nahiyar Asiya ba saboda ƙaramin raunin da ya ji a cinyarsa, kamar yadda kulob ɗin ya bayyana.

    Tuni ya bayyana wa kulob ɗin cewa yana son ya koma taka leda a wani wuri. Ya koma filin wasa na St James' Park a 2022 kan fan miliyan 60 daga Real Scieded ta Sifaniya.

  2. Newcastle ta yi watsi da tayin da Liverpool ta yi kan Isak

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙulob ɗin Newcastle United ya yi watsi da buƙatar Liverpool kan ɗan wasanta na gaba Alexander Isak.

    Newcastle dai ta ƙimanta darajar ɗan wasan ɗan asalin ƙasar Sweden a kan fam miliyan 150, inda ita kuma Liverpool tayin da ta yi kan ɗan wasan ya gaza kudin.

    Babu tabbaci dangane da haƙiƙanin kuɗin da Liverpool ta yi tayin ɗan wasan, sai dai akwai rahotonnin da e cewa kuɗin da ta taya ɗan wasan ya kai fam miliyan 110 ciki har da na sauran tsarbe-tsarabe.

    Kulob ɗin na Newcastle dai bai yi amfani da Alexender ba a lokacin rangadin da tawagar kulob ɗin ta yi a yankin Asiya, a daidai lokacin da yake neman damar ficewa - duk da cancantar da ƙungiyar wasan ta yi a wannan kakar ta gasar Champions League.

    Liverpool ta yi tayin ɗan wasan ne a lokacin da Isak ke atisaye shi kaɗai a tsohon kulob ɗinsa na Real Sociedad, yayin da ake tantamar yadda gaban ɗan wasan za ta kasance.

    Yanzu dai abin jira a gani shi ne ko Liverpool za ta ƙara yawan kuɗin tayin da ta yi kan ɗn wasan duk da cewa manajan ƙungiyar, Arne Slot ya zaƙu ya sanya sunan ɗan wasan a tawagarsa kafin sabuwar kakar wasannin.

  3. Tottenham na dab da cimma yarjejeniya kan ɗan Palhinha

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Tottenham na tattaunawa da Bayern Munich kan ba da aron ɗan wasan Portugal Joao Palhinha, mai shekara 30, yayinda suke kokarin ganin tsohon ɗan wasan tsakiya na Fulham ya koma Firimiya.

    RB Leipzig na cikin ƙungiyoyin da ke zawarcin Rasmus Hojlund kuma Manchester United na iya amfani da ɗan wasan mai shekara 22 na Denmark wajen musayarsa domin cimma yarjejeniya da ɗan wasan gaba a Slovenia, Benjamin Sesko mai shekara 22.

    Ɗan wasan Manchester United Jadon Sancho mai shekara 25, ya shirya karɓan albashin da za a zabtare masa kashi 50 cikin 100 na abin da yake samu domin koma taka leda a Borussia Dortmund.

    Ana saran Chelsea ta gabatar da tayi kan ɗan wasan Manchester United, Alejandro Garnacho, mai shekara 21, kafin a rufe kasuwar cinikin 'yan wasa. Karanta cikakken labarin a nan.

  4. Isak ya koma atasaye a Real Socieded

    Alexander Isak

    Asalin hoton, PA Media

    Ɗanwasan gab ana Newcastle Alexander Isak na can yana atasaye shi kaɗai a tsohuwar ƙungiyarsa ta Real Socieded, yayin da ake cigaba da cecekuce game da makomarsa a ƙungiyar kafin fara kakar wasa ta bana.

    Ɗanwasn na ƙasar Sweden mai shekara 25 bai samu shiga tawagar Newcastle da ta je nahiyar Asiya ba saboda ƙaramin rauni a cinyarsa kamar yadda kulob din ya bayyana.

    Isak na son ya bar Newcastle kuma ana kyautata zaton Liverpool ce kan gaba wajen neman ɗauke shi daga filin wasa na St James’ Park.

    Wata majiya ta shaida wa BBC cewa ɗanwasan na yin atsaye ne shi kaɗai a Socieded ba tare da sauran tsofaffin abokan wasansa ba.

    Ya koma Newcastle daga Socieded kan fan miliyan 60 a 2022.

  5. Nottingham Forest ta ɗauki Dan Ndoye daga Bologna

    Dan Ndoye

    Asalin hoton, Reuters

    Ƙungiyar Nottingham Forest ta kammala ɗaukar ɗanƙwallon Switzerland Dan Ndoye daga kulob ɗin Bologna ta Italiya.

    Ndoye ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekara biyar, abin da ya kawo ƙarshen zamansa a Italiya na shekara biyu.

    Ɗanwasan mai shekara 24 ya ci wa Bologna ƙwallo tara cikin wasa 41 a gasar Serie A da aka kammala.

    Shi ne ya ci ƙwallo ɗaya tilo a wasan ƙarshe na Coppa Italia da suka buga da AC Milan a watan Mayu, inda ya taimaka wa Bologna ɗaukar kofi na farko cikin shekara 50.

    "Lokaci ne mai daɗi kasancewata a Forest kuma nan take na ji ina so a yi wannan aikin da ni," a cewar Ndoye.

  6. Makomar Son na cikin rashin tabbas a Tottenham

    Son

    Asalin hoton, Getty Images

    Makomar kyaftin ɗin Tottenham, Son Heung-min, a kulob ɗin na cikin rashin tabbas yayin da ake tunkarar kakar bana.

    Saura wata 12 yarjejeniyar ɗanwasan gaban ta ƙare a ƙungiyar kuma rahotonni sun ce kungiyoyi da dama na sha'awar ɗaukar sa a Saudiyya da Amurka.

    Wakilin wasanni na BBC Sami Mokbel ya ce duk ma wani yunƙurin barin Tottenham zai faru ne bayan kammala balaguro a nahiyar Asiya.

    Ana kallon Son ɗan ƙasar Koriya ta Kudu a matsayin jigo wajen tallata harkokin kulob ɗin a nahioyar Asiya.

    Bayan wasa da suka buga da Arsenal a Hong Kong ranar 31 ga watan Yuli, sun wuce zuwa Koriya ta Kudun domin fafatawa da Newcastle United.

  7. Chelsea ta amince da ɗauko ɗanƙwallon Ajax Hato

    Jorrel Hato

    Asalin hoton, Getty Images

    Chelsea ta amince ta ɗauko ɗanƙwallon baya na Ajax, Jorrel Hato a kan fam miliyan 37, kamar yadda mahukunta ƙungiyar suka amince.

    Dan ƙwallon Netherlands ɗin mai shekaru 19, ya sanya hannu a yarjejeniyar shekaru bakwai har zuwa shekara ta 2032, kuma za a gwada lafiyarsa a London.

    Hato ya soma bugawa babbar tawagar Ajax kwallo a watan Fabarairun 2023 a matsayin ɗan shekaru 16.

    Kawo yanzu ya buga wasa 75 a cikin tawagar Ajax.

  8. Arsenal ta ɗauko ƴanƙwallo shida a kakar bana

    Viktor Gyokeres

    Asalin hoton, Arsenal/Facebook

    Arsenal ta kashe fiye da fam miliyan 191 wajen ɗauko ƴanƙwallon da za su taimaka mata a sabuwar kakar wasa ta 2025 zuwa 2026.

    Sannan kuma ta sayar da wadansu ƴanƙwallon.

    Ga jerin ƴanƙwallon da suka koma murza a filin Emirates:

    • Kepa Arrizabalaga - daga Chelsea a kan £5m
    • Martin Zubimendi - daga Real Sociedad a kan £60m
    • Christian Norgaard - daga Brentford - a kan £10m (zai iya zama £15m)
    • Noni Madueke - daga Chelsea - a kan £48.5m
    • Cristhian Mosquera - daga Valencia - a kan £13m
    • Viktor Gyokeres - daga Sporting - a kan £55m (zai iya zama £64m)
  9. Man United ta fara zawaracin Sesco daga RB Leipziig

    Sesco

    Asalin hoton, Getty Images

    Manchester United ta tuntuɓi RB Leipzig, kan sayen Benjamin Sesko domin ta kara karfin gurbin masu ci mata ƙwallaye.

    Ana ta alakanta Sesco da cewar zai koma Newcastle United da taka leda, bayan da ake tantama kan makomar Alexander Isak a bana a St James Park.

    Yanzu dai an samu yin tuntuɓa tsakanin United da RB Leipzig kan batun cinikin matashin mai shekara 22 ɗan wasan tawagar Slovenian.

    Sesco yana da damar barin gasar Bundesliga da zarar ya samu ƙungiyar da za ta saye shi kusan fam miliyan 70.

    Haka kuma United tana son yin zawarcin Ollie Watkins na Aston Villa, wadda tuni ta ce ba za ta sayar da mai shekara 29 ba.

  10. Arteta ya yaba wa Gyokeres da ya karɓi riga mai lamba 14

    Arsenal

    Asalin hoton, Getty Images

    Kociyan Arsenal, Mikel Arteta ya sanar ranar Laraba cewar ya jinjinawa sabon ɗan wasan da suka ɗauka Viktor Gyokeres kan karɓar riga mai lamba 14 - irin wadda gwarzon ɗan wasa, Thierry Henry ya saka.

    Ya bayyana hakan a lokacin da yake ganawa da ƴan jarida kan shirin wasan da Gunners za ta buga da Tottenham a Hong Kong a shirye-shiryen tunkarar kakar bana da za a fara a cikin watan Agusta.

    Kyaftin ɗin Gunners Martin Odegaard ya ce Gyokeres ya burge shi - kan yadda ya ci ƙwallaye a tsohuwar ƙungiyarsa, Sporting Lisbon da waɗanda ya zura a raga a lokacin atisaye a Arsenal.

    Gyokeres ɗan ƙwallon tawagar Sweden, shi ne na shida da Arsenal ta saya a bana bayan Noni Madueke da Kepa Arrizabalaga da Cristhian Mosquera da Christian Norgaard da kuma Martin Zubimendi.

  11. Shaw ya goyi da bayan gyare-gyaren da Amorim ke yi a Man United

    Shaw

    Asalin hoton, Getty Images

    Luke Shaw ya goyi da bayan yadda Ruben Amorim ke gyare-gyare a Manchester United.

    Mai shekara 30, shi ne mafi daɗewa a ƙungiyar Old Trafford, wanda ta ɗauka daga Southampton a 2014 a lokacin a matashin da ta saya mafi tsada a duniya.

    Shaw yana tare da koci na biyar da ta ɗauka da ya haura da United tare da ɗan wasan tawagar Ingila.

    United ta kare a mataki na 15 a kasan teburin Premier League a kakar da ta wuce da kasa lashe kofi, wadda Tottenham ta doke ta cinye Uefa Conference League.

  12. Gossip

    Asalin hoton, Getty Images

    Golan Ingila mai shekara 33 Nick Pope zai iya komawa Manchester United idan Newcastle ta yi nasarar ɗauko golan Southampton mai shekara 27, Aaron Ramsdale. (Talksport)

    Newcastle ta cimma matsaya da Southampton a kan ɗaukar Ramsdale a matsayin aro tare da zaɓin mallakarsa a ƙarshen kakar wasan nan. (Athletic - subscription required)

    Manchester United ta kuma shiga zawarcin golan PSG kuma ɗan asalin Italiya, Gianluigi Donnarumma, amma tana kaucewa shiga gogayyar ciniki da Chelsea da kuma Manchester City a kan ɗanwasan mai shekara 26. (Sun)

    Arsenal na ci gaba da zawarcin ɗanwasan tsakiyar Ingila Eberechi Eze, mai shekara 27, amma ba ta shirya biyan £60m kan ɗanwasan ba domin haka tana jira har sai Crystal Palace ta karya farashinsa. (Athletic - subscription required)

  13. Watakila Man United ta nemi sayen Pope na Newcastle

    Pope

    Asalin hoton, Getty Images

    Newcastle za ta fuskanci kalubale, bayan da ake ta raɗe-raɗi kan makomar mai tsaron ragarta, Nick Pope.

    Manchester United tana son zawarcin golan mai shekara 33 da zarar Newcastle ta kammala sayen Aaron Ramsdale daga Southampton kamar yadda Talksport ta sanar

    Yarjejeniyar Pope za ta kare a karshen kakr baɗi a St James Park, inda United ke son sayensa domin ya kalubalanci Andre Onana a Old Trafford.

  14. Rafli za su ɗaura kymara a jikinsu a gasar kofin duniya a 2026

    Ref

    Asalin hoton, Getty Images

    Alkalan tamaula za su ɗaura kyamara a jikinsu a lokacin gasar cin kofin duniya ta maza da za a buga a Amurka da Canada da Mexico a 2026.

    Tuni ƙungiyar ƙungiyoyin hukumomin ƙwallon kafa ta duniya IFAB ta amince da fasahar, bayan da aka yi amfani da tsarin a gasar Club World Cup da aka yi a Amurka a cikin watan nan.

    Manufar gwajin kyamarorin shi ne don ganin ko zai wadatar da yadda rafli ke ganin wasannin ta hanyar samar da hotuna da za su iya fayyace takaddama.

    An kuma amince cewar sauran gasar duniya za su iya amfani da fasahar har da lik-lik na kasahe.

    Kuma duk gasar dake son yin amfani da fasahar sai ta nemi izini daga IFAB da Fifa, waɗanda za su samar da fasahar da ilimim yadda za a yi amfani da ita domin a cimma buri.

  15. Trosaad

    Asalin hoton, Getty Images

    PSG ta ƙara ƙaimi domin kammala cinikin ɗanwasan bayan Bournemouth ɗan asalin mai shekara 22, Illia Zabarnyi. (Fabrizio Romano)

    Borussia Dortmund na bibiyar ɗanwasan tsakiyar Arsenal mai shekara 30, Leandro Trossard, ama akwai wasu ƙungiyoyin gasar Firimiya biyu da ke zawarcin ɗanwasan na Belgium. (Sky Sports Germany)

    Lyon na zawarcin ɗanwasan tsakiyar Ingila mai shekara 22, Tyler Morton, kuma tuni ta tuntuɓi Liverpool a kai. (Times)

    Everton ta mayar da hankali ga neman anwasan tsakiyar Juventus da Brazil mai shekara 27, Douglas Luiz. (GiveMeSport)

    Manchester City ta sanar da golan Jamus mai shekara 32, Stefan Ortega, cewa ba ta buƙatarsa a ƙungiyar bayan ta ɗauko James Trafford daga Burnley. (Fabrizio Romano)

  16. Granit Xhaka ya kammala komawa Sunderland

    Xhaka

    Asalin hoton, Getty Images

    An tabbatar da cewar Granit Xhaka ya koma Sunderland da taka leda daga Bayern Leverkusen.

    Ɗan wasan tawagar Switzerland, mai shekara 32 ya koma Sunderland kan yarjejeniyar kaka uku.

    Shin ina ya buga wasanni a baya?

    Ya fara da taka leda a FC Basel a matakin matashi daga makarantar horon tamaula ta ƙungiyar. ya kuma buga wa babbar ƙungiyar wasanni daga 2010 zuwa 2012 daga Borussia Monchengladbach.

    Daga nan ya koma Arsenal, wadda ya buga wa tamaula daga 2016 zuwa 2023. Ya lashe FA Cup biyu da Community Shields biyu.

    Xhaka ya koma wasa a Bayer Leverkusen, yana cikin ƴanwasan da suka lashe Bundesliga a karon farko a tarihin ƙungiyar a 2023/24.

    Ya buga wa tawagar Switzerland tamaula a karon farko daga 2011. Kawo yanzu ya yi mata karawa 137, ya kuma wakilci kasarsa a manyan gasa shida da yin ƙyaftin a 2024.

  17. Buchanan ya koma Villareal bayan kammala wasannin aro

    Kungiyar Villareal ta mallaki Tajon Buchanan kan yarjejeniyar kaka biyar, bayan da ya buga wasannin aro daga watan Fabrairu daga AC Milan.

    Buchanan, wanda ya taka leda a Inter a Janairun 2024 daga Club Brugge, ya buga wa Villareal wasa 13 a kakar da ta wuce.

    Kungiyar dake buga La Liga ta Sifaniya za ta fara wasa a gida ranar 15 ga watan gobe da Oviedo.

    Buchanan

    Asalin hoton, Getty Images

  18. Raducanu da Alcaraz za su buga karawar ƴanwasa bibiyu a US Open

    Tennis

    Asalin hoton, Getty Images

    An tabbatar da cewar Emma Raducanu da Carlos Alcaraz za a yi musu alfarmar shiga karawar ƴanwasa bibiyu a US Open.

    Za a fara wasannin daga watan gobe tun kan bude labulen gasar, inda za a bayar da ladan dalar Amurka miliyan daya ga wadanda za su lashe kofin, kimanin sama da naira biliyan daya da sama da naira miliyan 500.

    Raduna da Alcaraz suna daga cikin yan wasa bibiyu su shida da aka yi wa alfarmar shiga wasannin - akwai kuma karin biyu da za a sanar da za su, kenan za su kai su 16 da za su yi tata burza.

  19. James Trafford ya sake komawa Man City daga Burnley

    Trafford

    Asalin hoton, Getty Images

    Mai tsaron ragar tawagar Ingila, mai shekara 21, James Trafford ya sake komawa kungiyarsa ta Manchester City.

    Ya kuma rattaba hannu kan yarjejeniyar kaka biyar da kungiyar Etihad, wadda ya bari a 2023 ya koma Burnley.

    Trafford wanda zai sa riga mai lamba daya - ya zama na shida da City ta dauka a kakar nan bayan Rayan Ait-Nouri, Tijjani Reijnders da Marcus Bettinelli da Rayan Sherki da kuma Sverre Nypan.

    Trafford ya fara City daga 2015 daga nan aka bayar da aronsa ga Accrington da Bolton daga baya ya kasa samun buga wasanni a kungiyar Etihad saboda Ederson hakan ya sa aka sayar da shi kungiyar Turf Moor.

  20. Ko kunsan ƴanƙwallon da Liverpool ta ɗauko kawo yanzu ?

    Ekitike

    Asalin hoton, Liverpool/Facebook

    Liverpool ta kashe fam miliyan 265 wajen ɗauko ƴanƙwallon da za su taimaka mata a sabuwar kakar wasa ta 2025 zuwa 2026.

    Sannan kuma ta sayar da wadansu ƴanƙwallon biyar.

    Ga jerin ƴanƙwallon da suka koma Anfield:

    • Florian Wirtz – a kan £100m daga Bayer Leverkusen (zai iya zama £116m)
    • Hugo Ekitike – a kan £69m daga Eintracht Frankfurt (zai iya zama £79m)
    • Milos Kerkez – a kan £40m daga Bournemouth
    • Jeremie Frimpong – a kan £29.5m daga Bayer Leverkusen
    • Giorgi Mamardashvili – a kan £25m daga Valencia (zai iya zama £29m)
    • Armin Pecsi – a kan £1.5m daga Puskas Akademia
    • Freddie Woodman – daga Preston North End

    Waɗanda suka bar Anfield:

    • Luis Diaz – zuwa Bayern Munich a kan £65.5m
    • Jarell Quansah – zuwa Bayer Leverkusen a kan £30m (zai iya zama £35m)
    • Caoimhin Kelleher – zuwa Brentford a kan £12.5m (zai iya zama £18m)
    • Trent Alexander-Arnold – zuwa Real Madrid a kan £8.4m
    • Nat Phillips – zuwa West Brom a kan £1m (zai iya zama £3m)