Kyaututtuka uku da Tinubu ya yi wa ƴanmatan Najeriya da suka ci kofi

Bola Tinubu tare da kyaftin din Super Falcons a fadar shugaban Najeriya ranar 28 ga watan Yunin 2025

Asalin hoton, STATE HOUSE

Bayanan hoto, Bola Tinubu tare da kyaftin din Super Falcons a fadar shugaban Najeriya ranar 28 ga watan Yunin 2025
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Babbar tawagar ƙwallaon ƙafar mata ta Najeriya, Super Falcons ta koma gida bayan lashe gasar cin kofin ƙwallon ƙafar Afirka ta mata da aka gudanar a Morocco.

Tawagar ta isa Abuja, babban birnin Najeriya ne ranar Talata bayan nasarar da suka yi a wasan ƙarshe da aka yi a birnin Rabat, a ranar Asabar.

Falcons sun kafa tarihi bayan lashe kofin a karo na goma, bayan doke Morocco mai masaukin baƙi, wadda ba ta taɓa lashe gasar ba.

Bayan sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwae da ke Abuja, tawagar ta zarce kai-tsaye zuwa fadar shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu.

Bayan tarba ta ban-girma, Tinubu ya sanar da manyan kyaututtuka uku da ya yi wa ƴan wasan da masu horas da su:

Lambar girma ta OON

A lokacin da yake jawabi, Tinubu ya ce: "Na karɓi wannan kofi a madadin ƴan Najeriya, kuma zan ce muku: mun gode da wannan ƙwazo, saboda haka na karrama ƴan wasan da masu horas da su 11 da lamabar girmamawa ta Officer of the Order of the Niger (OON).

OON shi ne mataki na uku daga ƙasa a jerin lambobin girmamawa na Tarayyar Najeriya.

Gidaje masu ɗaki uku-uku

Baya ga lambar yabo, tukwuci na biyun da shugaban na Najeriya ya bai wa ƴan wasan shi ne na gidaje.

"Bugu da ƙari na bayar da umarnin a bai wa dukkanin ƴan wasa da masu horas da su gidaje masu ɗakuna uku-uku," in ji Tinubu a cikin jawabin nasa.

Bayanan bidiyo, Latsa hoton domin kallon yadda Super Falcons suka koma Abuja bayan lashe kofi

Dala 100,000

Daga nan ne kuma shugaban na Najeriya ya sanar da bai ƴan wasan kyautar tsabar kuɗi dala 100,000.

"Akwai kyautar kudin naira kwatankwacin dala 100,000 ga kowace ƴar wasa 24 da kuma dala 50,000 ga tawagar masu horaswa."

Hakan na nufin ƴan wasan za su tashi da kyautar kuɗi kimanin naira miliyan 150.

...

Asalin hoton, Ministry of Sports, Nigeria

Shugaba Tinubu da mai ɗakinsa Remi Tinubu da wasu daga cikin ƴan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta mata ta Najeriya, Super Falcons a fadar shugaban ƙasa

Asalin hoton, STATE HOUSE

Bayanan hoto, Shugaba Tinubu da mai ɗakinsa Remi Tinubu da wasu daga cikin ƴan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta mata ta Najeriya, Super Falcons a fadar shugaban ƙasa
Bola Tinubu tare da tawagar Super Falcons da masu horas da su a fadar shugaban ƙasa ranar 28 ga watan Yulin 2024

Asalin hoton, STATE HOUSE

Bayanan hoto, Bola Tinubu tare da tawagar Super Falcons da masu horas da su a fadar shugaban ƙasa ranar 28 ga watan Yulin 2025