Hamas ta yi watsi da tayin Isra'ila na tsagaita wuta

Hamas

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

A hukumance, Hamas ta yi watsi da tayin Isra'ila na tsagaita wuta, tana mai cewa a shirye take a tattauna sabon shirin da zai kai ga sakin dukkan mutanen da take tsare da su, da kawo ƙarshen yaƙin baki ɗaya da kuma sako Falasɗinawan da Isra'ilan ke tsare da su a matsayin fursunoni.

Wani saƙon bidiyo da babban mai shiga tsakani daga ɓangaren Hamas a tattaunawar da ake yi, Khalil al-Hayya, ya fitar ya ce: "Ba za mu amince da duk wata yarjejeniyar wucin gadi da zata cika muradun siyasar firaiministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ba."

Mutane 59 ne suka rage a hannun Hamas, kuma ana kyautata zaton 24 daga cikin su suna raye.

Tayin baya bayan nan da Isra'ila ta gabatar a tattaunawar tsagaita wutar ta ƙunshi dakatar da hare-hare na kwana 45 da kuma sako 10 daga cikin mutanenta da Hamas ke tsare da su.

Ministan kuɗn Isra'ila nai tsattsauran ra'ayi Bezalel Smotrich ya ce lokaci ya yi da za a "Aika da Hamas lahira".

Dama tun a farkon mako jami'an Hamas suka nuna wa BBC alamun ba za su amince da tayin Isra'ilan na tsagaita wuta ba.

"Netanyahu da gwamnatinsa na amfani da tsagaita wutar wucin gadi wajen cimma muradun su na siyasa domin ci gaba da yaƙin da kuma jefa mutane cikin ƙangin yunwa. Kuma ba su damu ba ko da kuwa hakan na nufin sun sadaukar da dukkan mutanensu daake tsare da su," in ji Hayya.

Ya ƙara da cewa Hamas a shirye take ta amince da yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin baki ɗaya da sharaɗin sako mutanen da take tsare da su, da kuma sako mata nata mutanen da ke zaman gidan yari a Isra'ila.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Hamas ta taɓa bayyana cewa a shirye take ta ƙulla duk wata yarjejeniya da za ta kawo ƙarshen yaƙin baki ɗaya, amma da alama ɓangarorin biyu ba su kama hanyar cimma hakan ba.

Isra'ila dai ta ce burin ta shi ne raba Hamas da duk makamanta da kuma rushe ƙungiyar baki ɗaya.

A halin yanzu dai gomman mutanen Gaza ake kashewa a kowacce rana a hare-hare ta sama, kuma babu wani tallafi da ke shiga Zirin Gazan.

Ma'aikatar lafiya ta Hamas ta ce harin baya bayan nan ya kashe mutum 37 kuma mafi yawan su suna zaune ne sansanin fararen hula ƴan gudun hijira.

Shedu a al-Mawasi sun ce Falasɗinawa da yawa, ciki harda ƙananan yara sabon harin Isra'ila ya kashe.

"Da gudu na leƙa waje kuma na ganewa idanu na yadda wuta ta tashi a sansanin'' In ji wani mazaunin Gaza.

Dakarun Isra'ila ba su yi martani da gaggawa ba, kuma ko a lokacin da suka yi cewa su kayi za su gudanar da bincike.

Isra'ila dai ta buƙaci Falasɗinawa su fice daga sauran sassan Gaza su kuma koma al-Mawasi da zama.

Dakarun Isra'ila sun ce hare-haren nasu suna faɗawa ne a kan maɓoyar mayaƙan Hamas.

An fara yaƙin ne a ranar 7 ga watan Oktoban 2023 lokacin da Hamas ta kai hari cikin Isra'ila inda ta kashe mutane aƙalla 1,200 da yin garkuwa da wasu 251.

Ma'aikatar lafiya ta Hamas ta ce mutanen da Isra'ila ta kashe daga fara yaƙin zuwa yanzu sun kai 51,065.