Ƙalubalen da shugabannin hukumar INEC suka fuskanta a shekaru 27

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar zaɓe ta Najeriya mai zaman kanta INEC ta samu shugabanni guda shida tun bayan komawar ƙasar turbar dimokraɗiyya a 1999.
Kuma tun daga jamhuriyar ta huɗu kawo yanzu, hukumar ta INEC na fuskantar matsaloli daban-daban da suka hada da tsoma bakin ƴan siyasa da ƙalubalen shari'a da na tsaro da matsalolin kayan aiki da ma ƙarancin kuɗaden gudanarwa.
To sai dai za a iya cewa kowane shugaban daga cikin shugabanni shida da suka jagoranci hukumar na da irin nasa keɓantattun matsalolin da ya yi fama da su bayan na gama-gari.
BBC ta yi nazari dangane da irin matsalolin da kowanne daga cikin shugabannin Inec ɗin ya fuskanta a tsawon zamanin da ya jagoranci hukumar.
Farfesa Joash Amoputan - Oktoba 2025

Asalin hoton, Facebook/INEC
A watan oktoban 2025 ne shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya nada Farfesa Joash Amupitan a matsayin shugaban hukumar zaɓen Najeriya INEC, bayan ƙarewar wa'adin Farfesa Mahmood Yakubu wanda ya shugabanci hukumar na tsawon shekara 10.
Saɓanin sauran shugabannin hukumar da suka gabace shi, Farfesa Amoputan ya fara da fuskantar manyan ƙalubale tun daga ranar da aka naɗa shi, inda shugabannin jam'iyyun ƙasar da na addinai da kuma sauran al'umma suka yi ta sukan sa.
- Sarƙaƙiyar shari'o'i
Za a iya cewa babban ƙalubalaen da Farfesa Amupitan yake fuskanta shi ne sarƙaƙiyar da ke cikin shari'o'i da suka shafi jam'iyyu wani abu da ke hargitsa tunanin INEC.
A makon da ya gaba ne wata babbar kotun tarayya a Lokoja jihar Kogi ta umarci hukumar INEC da ta cire jam'iyyar NDC daga jerin jam'iyyun da za su shiga zaben 2027, al'amarin da ya janyo taƙaddama da ruɗuni.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ita ma jam'iyyar hamayya ta ADC ta shiga ruɗani bayan da hukumar zaɓe ta INEC ta bayyana cewar Sanata David Mark ba shi ne shugaban jam'iyyar ADC ba sakamakon wani hukuncin kotu da ya nemi a yi hakan sakamakon rikicin ɓangaren David Mark da na Nafi'u Gombe.
Su ma sauran jam'iyyun ƙasar na hamayya kamar PDP da LP suna fuskantar rigimar shari'a inda ɓangarori biyu na jam'iyyar suka fitar da ƴan takarar shugaban ƙasa da mataimaki.
- Lambar sirri ta shigar da sunayen ƴan takara
Batun bai wa jam'iyyun siyasa lambar sirri da za ta ba su damar shigar da sunayen ƴan takararsu da za su tsaya zaɓen 2027, shi ma ya janyowa hukumar cancakwata.
Da farko hukumar ta Inec dai ta ce za ta bayar da lambobin sirrin a ranar 26 ga watan Yuni amma kuma hakan ba ta samu ba, inda Inec ta ce za ta saki lambobin sirri ranar Litinin.
- Ƙorafin ƙungiyoyin addini
Majalisar Ƙoli ta Addinin Musulunci ƙarƙashin jagorancin Dr Bashir Umar ta nuna takaicinta ga matsayar Gwamnatin Tarayya na ƙin sauraren ƙungiyoyin musulmai na neman a sauke Farfesa Amupitan daga muƙaminsa.
SCSIAN ta ce Amoputan yana daga cikin mutanen da suka "rubuta wasiƙa ga Amurka" wadda ta kai ga ayyana Najeriya a matsayin ƙasar da "ake kashe Kiristoci".
- Zargin kasancewarsa ɗan APC
A ranar Juma'a 11 ga watan Afrilu fitaccen marubucin nan mai tarin mabiya a kafafen sada zumunta mai yawan janyo ce-ce-ku-ce Farfesa Farooq Kperogi ya wallafa wani abu da 'yan Najeriya suka kalla a matsayin tonan asiri ga shugaban na INEC Farfesa Amupitan.
A shafinsa na X Farfesa Kperogi ya wallafa cewa bayan bin diddigi na shekara da shekaru na wallafe-wallafen da Amupitan ya yi a shafinsa na X ya gano cewa mutumin da aka nada ya jagoranci INEC "dan jam'iyyar APC ne" kuma mai goyon bayan shugaba Tinubu.
Kperogi ya yi ta bin ƙwaƙƙwafin bayanan da shugaban na INEC ya riƙa wallafawa masu alaƙa da shugaban Najeriya Tinubu.
Sai dai kuma hukumar INEC ta bayyana al'amarin da ƙagaggun labaran ƙarya da ake yaɗawa game da shugaban hukumar Farfesa Amupitan, inda ta nemi ƴan Najeriya da su yi watsi da bayanan.
Farfesa Mahmud Yakubu, 2015 - 2025

Asalin hoton, Getty Images
A ranar 9 ga watan Nuwamban 2015 ne tsohon shugaban Najeriya, marigayi Muhammadu Buhari ya naɗa Farfesa Mahmud Yakubu a matsayin shugaban hukumar zaɓen ƙasar, INEC bayan kammalar wa'adin Farfesa Attahiru Jega.
A tsawon shekaru 10 da ya kwashe, Yakubu ya fuskanci manyan ƙalubale da dama kamar haka:
- Yawan Shari'o'in zaɓe da rikicin kotu: Inec ta yi fama da dubban ƙararrakin zaɓe a kotuna sakamakon yadda ake samun hukunce-hukunce masu karo da juna wanda ya rinƙa jefa INEC cikin ruɗani.
- Katsalandan: Inec ta fuskanci katsalandan daga ƴan siyasa da hukumomi wani abu da ya sa ƴan Najeriya suka yi shakku dangane da sahihancin zaɓen.
- Matsalolin na'urorin zaɓe: An sha fama da na'urori kamar BVAS na tantance masu zaɓe da IReV na tura sakamakon zaɓe kai tsaye. Wannan ya janyo ƴan ƙsar yanke ƙauna kan samun sahihin zaɓe.
- Matsalolin kayan aiki da rashin shirye-shirye: Hakan ta sa aka rinƙa samun jinkirin fara zaɓe da ɗage wasu zaɓuka.
- Matsalolin tsaro da tashin hankali: An samu lokutan da aka rinƙa ƙaddamar da hare-hare kan ofisoshi da ma'aikatan hukumar zaɓe inda ake lalata kayan zaɓe.
Farfesa Attahiru Jega, 2010 - 2015

Asalin hoton, Getty Images
Farfesa Attahiru Jega ya zamo shugaban hukumar zaɓen Najeriya, INEC a lokacin mulkin tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan a 2010.
Jega ya kwashe shekaru biyar yana jagorancin hukumar inda ya gudanar da manyan zaɓukan ƙasar guda biyu wato na 2011 da 2015.
Kamar sauran shugabannin hukumar, shi ma farfesa Jega ya fuskanci matsaloli a zamaninsa.
- Katsalandan: Inec ta fuskanci katsalandan daga ƴan siyasa da hukumomi wani abu da ya sa ƴan Najeriya suka yi shakku dangane da sahihancin zaɓen. Ko da a lokacin tattara sakamakon zaɓen 2015, sai da aka samu wasu jami'an gwamnati da suka so hana aikin tafiya yadda ya kamata.
- Ɗage zaɓe: Hukumar zaɓe a ƙarƙshin Farfesa Jega ta yi fama da matsalar ɗage zaɓuka sakamakon matsalolin kayan aiki da suka hada da sabuwar na'urar da aka fito da ita Card reader mai tantance masu zaɓe.
- Rikicin zaɓe: Zaɓukan 2011 sun haifar da tashin hankali bayan bayyana zaɓe a wasu jihohin ƙasar al'amarin da ya haifar da rasa rayuka da dukiyoyi.
- Matsalar tsaro: Haka kuma, a lokacin shirye-shiryen zaɓen 2015, akwai barazanar Boko Haram a Arewa maso gabas.
- Shari'o'i: Bayan zaɓe, jam'iyyu da 'yan takara sun kai ƙara kotu, wani abin da ya nuna yadda ake fuskantar rashin gamsuwa da sakamakon zaɓen.
Amina Zakari, Yuli - Nuwamba 2015
Amina Bala Zakari ta jagoranci hukumar zaɓen Najeriya a matsayin riƙon ƙwarya tsakanin 30 ga Yulin 2015 zuwa 9 ga watan Nuwamban 2015, bayan ƙarewar wa'adin Farfesa Attahiru Jega, kafin naɗa Farfesa Mahmud Yakubu.
Amina Zakari ta yi shugabanci na ɗan lokaci kaɗan, wanda ya sa ba ta da isasshen lokaci don aiwatar da manyan sauye-sauye inda ta fi mayar da hankali kan ci gaba da tsarin da ta gada daga Farfesa Jega.
Maurice Iwu, 2005 - 2010
Tsohon shugaban Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo ne ya naɗa Farfesa Maurice Iwu a matsayin wanda zai jagoranci hukumar zaɓen ƙasar mai zaman kanta daga watan Yunin 2005 zuwa Afrilun 2010.
Shi ma kamar sauran wadanda suka zo bayansa, Farfesa Iwu ya fuskanci matsaloli da suka dabaibaye jagorancinsa na shekara biyar.
- Zarge-zargen maguɗi a zaɓen 2007: Zaɓen 2007 shi ne mafi girman ƙalubalen da ya fuskanta ciki har da satar ƙuri'a da sauya sakamako da rashin gaskiya wajen gudanar da zaɓuka. Ƙungiyoyin sa ido na cikin gida da na ƙasashen waje sun bayyana zaɓen a matsayin mai cike da kura-kurai. Sauran matsalolin sun haɗa da:
- Matsin lamba daga 'yan siyasa:
- Yawan shari'o'i bayan zaɓe
- Rashin ingantaccen tsarin gudanarwa
- Suka daga ƙasashen waje da masu sa ido
Abel Guobadia, 2000 - 2005
Sir Abel Guobadia ne ya jagoranci babban zaɓen shekarar 2003, wanda tsohon shugaban Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya yi nasarar yin tazarce.
To sai dai shi ma kamar sauran waɗanda suka jagoranci hukumar zaɓen mai zaman kanta ya fuskanci matsalolin irin na lokacin kamar haka:
- Katsalandan daga ƴan siyasa: A a karshen wa'adinsa, Sir Abel ya faɗi cewa ba a bar hukumar ta yi aikinta ba saboda katsalandan daga jami'an gwamnati.
- Kura-kuran zaɓe: Masu saka ido na ciki da waje sun bayyana zaɓen 2003 da mai cike da kura-kurai:
- Rashawa da cin hanci: Abel da kansa ya sha faɗin cewa an samu rashawa da cin hanci a ɓangaren jami'ai da ma'aikatan hukumar zaɓe.
- ƙararrakin daga ƙungiyoyin siyasa: Kamar shugaban hukumar na yanzu, shi ma Abel ya yi fama da ƙungiyoyin siyasa da suka yi shigar da hukumar ƙra a kotunan bisa neman a yi musu rijista.
Ephraim Akpata, 1998 - 2000
Ephraim Omorose Ibukun Akpata ya zama shugaban hukumar zaɓe a lokacin mulkin tsohon shugaban soji, Janar Abdussalam Abubakar, tsakanin daga shekarar 1998 har zuwa watan Janairun 2000.
A ƙarƙshin mista Ephraim ne aka yi wa jam'iyyu 9 rijista daga ƙungiyoyin siyasa 26 da suka nemi rijistar wanda ya share fagen babban zaɓen 1999.
Matsalolin da mista Ephraim ya fuskanta sun haɗa da:
- Gajeren lokaci na shirya zaɓe.
- Rashin ingantacciyar rijistar masu zaɓe.
- Matsalolin kayan aiki.
- Rashin amincewar jama'a.
- Katsalandan da matsin lamba daga sojoji da ƴan siyasa.












