Me ya sa Amurka ta janye sojojinta daga Najeriya?

Sojojin Amurka

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Amurka ta janye mafi yawan sojojin da ta tura Najeriya domin wani aikin haɗin gwiwa na yaƙi da ta'addanci a yankin Tafkin Chadi, amma ta ce haɗin gwiwar tsaro tsakaninta da Najeriya zai ci gaba.

A farkon wannan shekara, Amurka ta sanar da tura kimanin sojoji 200 zuwa ƙasar domin tallafa wa ƙoƙarin Najeriya na yaƙi da masu tayar da ƙayar baya ta hanyar horaswa da musayar bayanan sirri da kuma haɗin gwiwar soji, tare da jaddada cewa sojojinta ba za su shiga filin daga ba.

Da yake magana da manema labarai a ranar Alhamis, Kwamandan Rundunar Sojin Sama ta Amurka a Afirka, Janar Dagvin Anderson, ya ce ƙasashen biyu za su ci gaba da musayar bayanan sirri tare da tallafa wa ayyukan yaƙi da mayaƙan ƙungiyar IS.

Ya ce aikin da aka gudanar a yankin Tafkin Chadi ya taimaka wajen tarwatsa hanyoyin sadarwar IS har zuwa wajen Najeriya, lamarin da ya ƙara ƙarfi ga ƙoƙarin da ake yi a duniya wajen yaƙar ƙungiyar.

'Mun magance kisan Kiristoci a Najeriya'

Matakin na zuwa ne bayan da a baya-bayan nan Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce Amurka ta magance matsalar abin da ya kira kisan kiyashin Kiristocin Najeriya.

A nasa ɓangare Janar Anderson ya ce "Mun janye mafi yawan dakarunmu da aka tura musamman domin wannan aiki, amma muna ci gaba da haɗin gwiwar da Najeriya da nema domin tabbatar da ci gaba da musayar bayanan sirri da kuma fahimtar da ake buƙata wajen gudanar da waɗannan ayyuka masu wahala."

Wannan sanarwa ta zo ne bayan watanni na ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar soji tsakanin ƙasashen biyu.

Jami'an Najeriya da na Amurka sun ce musayar bayanan sirri ta taimaka wa dakarun Najeriya wajen kashe ɗaya daga cikin manyan shugabannin ƙungiyar IS ta duniya da kuma sama da mayaƙan jihadi 200 a yayin hare-haren haɗin gwiwa ta sama da ƙasa a arewa maso gabashin Najeriya.

Janar Anderson ya ce an yi wa jagorancin IS a Najeriya mummunar illa sosai, inda ya yi iƙirarin tarwatsa tsarin jagorancin ƙungiyar a cikin ƙasar tare da hanyoyin sadarwarta na duniya baki ɗaya, lamarin da ya rage mata damar sadarwa da gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.

Ya ce dakarun Najeriya sun ci gaba da gudanar da hare-hare tun bayan aikin haɗin gwiwa da aka yi a watan Mayu, inda suke kai hare-hare kan sansanonin IS.

Ya kuma ƙara da cewa wannan yaƙin ya sa an samu ƙaruwar mayaƙan IS da suka miƙa wuya a arewa maso gabashin Najeriya.

Kwalliya ta biya kuɗin sabulu?

Dr Audu Bulama Bukarti, mai sharhi kan lamuran tsaro a nahiyar Afirka, ya shaida wa BBC cewa, ya na ganin kai tsaye ba za a ce kwalliya ta biya kuɗin sabulu ba a game da zaman sojojin a Najeriya.

Ya ce, "A gaskiya na dauka sojojin za su dauki lokaci mai tsayi a Najeriya, saboda sun ce sun zo domin taya Najeriya yaki da kungiyar Boko Haram, to amma mu a iya abin da muka sani babban aikin da suka yi a game da yaki da Boko Haram, kwalli daya daya ne tal, shi ne kashe Abu Bilal al Mainoki tare da wasu mukarrabansa."

"Kisan da aka yi wa wadannan 'yan Boko Haram din babban ci gaba ne kuma koma baya ne ga 'yan kungiyar," in ji shi.

Bukarti, ya ce,"mu a zatonmu shi ne su waɗannan sojoji na Amurka za su ci gaba da irin wadannan ayyuka har sai an gurgunta kungiyar Boko Haram kafin su ce sun janye."

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ya ce "a gaskiya daga mahangar Najeriya za a iya cewa kwalliya ba ta biya kuɗin sabulu ba, to amma da an ce sun ci gaba da zama har sai an ci karfin 'yan Boko Haram da 'yan bindiga, to za a iya cewa kwalliya ta biya kudin sabulu."

"To amma daga bangaren Amurka fa, kwalliya ta biya kudin sabulu, domin tun daga lokacin da suka ce za su shigo, muka ce dama a wajen shugaban kasar siyasa ce don bukatarsa ta biya," in ji shi.

Masanin tsaron ya ce, "Yanzu ni ina ganin tun da sojojin na Amurka za su fice daga Najeriya, to abin da ya kamata shi ne, shi ne ita Amurkan da kawayen Najeriya wato kasashen yamma su sayar wa da Najeriya kayan aikin da ta ke bukata wajen yakar ta'addancin, sannankuma idan akwai wata kwarewa da suke da ita wadda babu a Najeriya to su taimaka."

Tun a watan Fabrairun 2026 ne, Amurka ta sanar da shirin tura sojoji 200 zuwa Najeriya domin horas da dakarun ƙasar dabarun yaƙi da ƙungiyar masu tayar da ƙayar baya.

Matsalar tsaron da Najeriya ke fuskanta galibi hare-hare ne na sari-ka-noƙe ko yaƙin sunƙuru.

Galibi ƙungiyoyin ƴanbindigar da ke addabar Najeriya na da mafaka ne cikin dazuka ko tsaunuka ko ma cikin tafki, kamar Tafkin Chadi da ake tunanin Boko Haram da ISWAP na ciki.

Ita kuwa rundunar sojin Amurka na da ƙwarewa sosai a wannan fanni, domin suna shiga wurare masu sarƙaƙiya su kuma yi nasara.