KAI TSAYE, Jana’izar Khamenei da sauran abubuwan da ke faruwa a duniya 04/07/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwa kan Jana’izar Khamenei da sauran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Asabar 4 ga watan Yulin 2026

Skip Bidiyo and continue reading
  • Zanga-zanga a aAfirka ta Kudu
  • xxx
  • Ummulkhairi Aliyu
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Arsenal
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Kutama
  • xxx

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Isiyaku Muhammad

  1. Iran ta gargaɗi Birtaniya da Faransa kan duk wani matakin soji a mashigar Hormuz

    ....

    Asalin hoton, Tasnim news agency

    Mataimakin ministan harkokin wajen Iran, Kazem Gharibabadi, ya gargaɗi Birtaniya da Faransa kan duk wani yunƙurin tura sojoji zuwa mashigan Hormuz, yana mai cewa hakan zai haifar da mummunan sakamako.

    Gargaɗin nasa ya zo ne bayan wata sanarwar haɗin gwiwa da ƙasashen biyu suka fitar, inda suka bayyana Mashigar Hormuz a matsayin muhimmin hanyar sufuri ga tattalin arzikin duniya, tare da nuna shirinsu na taimakawa wajen tabbatar da tsaron jiragen ruwa da ke bi ta yankin.

    A wani saƙo da ya wallafa a dandalin X, Gharibabadi ya ce Hormuz ba wurin nuna ƙarfin soji ba ne ga ƙasashen da ba sa yankin, yana mai jaddada cewa Iran ce ke da alhakin tabbatar da tsaron mashigar tare da sauran ƙasashen da ke gaɓar ruwan yankin.

    Ya ƙara da cewa duk wani matakin soji da ƙasashen waje za su ɗauka a yankin zai fuskanci martani, yana mai cewa waɗanda suka haddasa rikici ne za su ɗauki alhakin duk wani sakamako da ka iya biyo baya.

  2. INEC ta ƙara wa'adin rajistar masu zaɓe zuwa 26 ga Yuli

    ....

    Asalin hoton, INEC/X

    Hukumar zaɓen Najeriya mai zaman kanta INEC ta sanar da ƙara wa'adin ci gaba da rajistar masu zaɓe na tsawon makonni biyu, domin bai wa 'yan Najeriya da suka cancanta ƙarin damar yin rajista.

    A wata sanarwa da Kwamishinan Hukumar Mohammed Kudu Haruna, ya sanya wa hannu, INEC ta ce ta ɗauki matakin ne bayan nazarin yadda aikin rajistar ke gudana da kuma la'akari da ra'ayoyin da ta samu daga ofisoshinta na jihohi, jam'iyyun siyasa, ƙungiyoyin farar hula da sauran masu ruwa da tsaki.

    Hukumar ta bayyana cewa aikin rajistar wanda ya fara a ranar 18 ga Agustan 2025, kuma aka shirya kammala shi a ranar 10 ga Yulin 2026, yanzu zai ci gaba har zuwa ranar Lahadi 26 ga Yulin 2026.

    INEC ta kuma sanar da ƙaddamar da tsarin rajistar kai tsaye ta intanet ga masu yin rajista karo na farko.

    Hukumar ta ce daga ranar 8 ga Yulin 2026, masu son yin rajista za su iya amfani da shafinta na intanet domin kammala rajistar.

  3. 'Mojtaba Khamenei ba zai jagoranci sallar jana'izar mahaifinsa ba'

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Kafofin yaɗa labaran Iran sun ce Mojtaba Khamenei ba zai jagoranci sallar jana'izar mahaifinsa, Ayatollah Ali Khamenei ba, yayin da aka bayyana sunayen manyan malamai da za su jagoranci sallolin jana'izar a birane daban-daban.

    Kamfanonin dillancin labaran Iran sun ruwaito cewa Ayatollah Jafar Sobhani Tabrizi ne zai jagoranci sallar jana'izar a Tehran, yayin da Ayatollah Nasser Makarem Shirazi zai jagoranta a Qom, sannan Ayatollah Hossein Nouri Hamedani zai jagoranta a Mashhad.

    Sakataren kwamitin shirya jana'izar Ali Khamenei, Ali Akbar Pourjamshidian, ya ce batun halartar Mojtaba Khamenei jana'izar mahaifinsa na hannun ofishin jagorancin addini ne, kuma idan aka cimma matsaya za a sanar da jama'a ta hanyar ofishinsa.

    Mojtaba Khamenei bai fito bainar jama'a ba tun bayan fara yaƙin da ya yi sanadin mutuwar mahaifinsa da wasu daga cikin 'yan uwansu a farkon rikicin.

    Har yanzu kuma ba a saki wani sautin murya ko bidiyonsa ba tun bayan fara yaƙin.

  4. Iran ta kama mutum shida bisa zargin tayar da hankalin Jama'a

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Dakarun juyin juya halin Iran a lardin Tehran sun sanar da kama mutum shida a gundumar Pardis.

    A cewar wata sanarwa da hukumar ta fitar, an kama mutanen ne bisa zargin suna da alaƙa da abin da ta kira "ƙungiyoyin masu adawa da juyin juya hali" tare da aikata ayyukan da ke "tayar da hankalin jama'a."

    Hukumar ta ce kamen ya biyo bayan sa ido na tsawon lokaci da jami'an leƙen asirinta suka yi a manhajojin Telegram da Instagram, tare da tattara bayanan da suka kai ga gano waɗanda ake zargin.

    Sai dai sanarwar ba ta bayyana ƙarin bayani kan ainihin ayyukan da ake zargin mutanen da aikatawa ba, ko kuma matakan shari'ar da za a ɗauka a kansu.

  5. Sojojin Najeriya sun daƙile yunƙurin satar mutane tare da kashe 'ɗan ta'adda a Benue

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun daƙile wani yunƙurin satar mutane a ƙauyen Jotar da ke kusa da shingen binciken ababen hawa na Quarantine a Jihar Benu tare da kashe 'ɗan ta'adda.

    A wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce dakarunta sun kaddamar da samamen ne bayan samun sahihan bayanan sirri a ranar 2 ga Yulin 2026, lamarin da ya sa jami'an tsaron da ke yankin suka yi gaggawar kai ɗauki

    Sanarwar ta ce da isar dakarun wurin, sun yi artabu da maharan waɗanda suka buɗe musu wuta, lamarin da ya haifar da musayar harsasai.

    A sakamakon arangamar, an kashe mutum guda da ake zargin ɗan ta'adda ne, yayin da aka ƙwato bindiga ƙirar AK-47 da kuma kwanson harsasai guda biyu.

    Rundunar ta ce akwai alamun cewa wanda aka kashe na iya kasancewa cikin gungun masu laifi da suka kai hari kan matafiya a ranar 1 ga Yul.

  6. Houthi ta yi barazanar kai hari kan filayen jiragen sama a Saudiyya

    Ƙungiyar Houthi ta Yemen ta yi barazanar kai hare-hare kan filayen jiragen sama da sauran muhimman wurare a Saudiyya idan Riyadh ta ci gaba da abin da ta kira ƙeta sararin samaniyar Yemen.

    Kakakin rundunar Houthi, Yahya Saree, ya ce mayaƙansu sun fuskanci jiragen yaƙin Saudiyya da suka yi ƙoƙarin hana wani jirgin saman farar hula na Iran sauka a filin jirgin saman Sanaa.

    Ya kuma jaddada cewa zirga-zirgar jirage tsakanin Sanaa da Tehran za ta ci gaba.

    Tashar Al-Masirah mai alaƙa da Houthi ta ruwaito cewa wani jirgin Iran ya isa Sanaa a ranar Juma’a ɗauke da wakilan ƙungiyar da suka halarci jana'izar tsohon jagoran Iran, Ali Khamenei, tare da sama da marasa lafiya 200.

    A martaninta, ƙawancen sojojin da Saudiyya ke jagoranta ya ce kalaman Houthi wani yunƙuri ne na kau da hankali daga abin da ya kira ayyukan ƙungiyar a Yemen, tare da yin gargaɗin cewa zai mayar da martani mai ƙarfin da ba a taɓa gani ba ga duk wani hari kan Saudiyya.

  7. 'Sama da ƴan gudun hijira 640,000 sun koma gidajensu a Lebanon'

    .....

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar Kula da Ƙaura ta Duniya (IOM) ta bayyana cewa sama da mutum 640,000 da rikicin ya raba da muhallansu a Lebanon sun koma gidajensu bayan raguwar faɗace-faɗace da kuma yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a yankin Gabas ta Tsakiya.

    Sai dai ƙungiyar ta ce har yanzu kusan mutum 500,000 na ci gaba da ƙaura, ba tare da sun samu damar komawa gidajensu ba.

    Rahoton ya dogara ne kan bayanan da aka tattara tun daga ranar 22 ga watan Yuni tare da haɗin gwiwar hukumomin yankin.

    Lebanon ta faɗa cikin rikicin yankin a farkon watan Maris lokacin da ƙungiyar Hezbollah mai samun goyon bayan Tehran ta harba makamai masu linzami zuwa Isra'ila, bayan kashe jagoranaddinin Iran a hare-haren haɗin gwiwar Amurka da Isra'ila.

    A martaninta, Isra'ila ta ƙaddamar da hare-haren sama da kuma farmaki ta ƙasa a kudancin Lebanon.

    Jami'an Lebanon sun ce hare-haren Isra'ila sun kashe kusan mutum 4,300 tare da raba fiye da mutum miliyan ɗaya da gidajensu, musamman a kudancin ƙasar da kuma kudancin unguwannin Beirut.

  8. Za a yi wa gawar Khamenei sallar jana'iza ranar Lahadi

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Mahukuntan Iran sun sanar da cewa za a yi wa gawar Ayatollah Ali Khamenei sallar jana'iza da safiyar Lahadi a harabar Mosalla da ke birnin Tehran.

    A cewar sanarwar da kafafen yaɗa labarai na Iran suka wallafa, za a gudanar da sallar ne da ƙarfe shida na safe, a wani ɓangare na bukukuwan jana'izar da ake yi wa tsohon jagoran addinin ƙasar.

    Sai dai sanarwar ba ta bayyana sunan wanda zai jagoranci sallar jana'izar ba.

    A halin yanzu ana ci gaba da zaman makoki da bukukuwan jana'izar Khamenei, waɗanda aka tsara za su gudana na tsawon kwanaki shida tare da halartar dubban masu makoki daga sassa daban-daban.

  9. Magoya bayan Ali Khamenei na kiran ɗaukar fansa

    .....

    Asalin hoton, Getty Images

    Dubban magoya bayan Ayatollah Ali Khamenei sun taru a harabar Mosalla da ke Tehran, inda suka rika kiran a ɗauki fansa yayin da aka fara jana'izarsa.

    A cewar AFP, wasu daga cikin mahalartan sun ɗaga jajayen tutoci da alluna masu ɗauke da saƙonnin kira ga ɗaukar fansa, tun kafin isowar akwatin gawarsa wurin taron.

    Rahotanni sun ce masu makokin sun rika rera taken “Mutuwa ga Amurka” da kuma “Ramuwar gayya, ramuwar gayya”, suna bayyana buƙatar mayar da martani.

    Jana'izar, wadda aka shirya za ta gudana na tsawon kwanaki shida, ta kuma samu halartar manyan jami'ai da wakilai daga ƙasashen yankin, yayin da mahukuntan Iran ke sa ran miliyoyin mutane za su shiga cikin bukukuwan makokin da za a gudanar a Iran da Iraq.

  10. An Fara Jana'izar Ayatollah Khamenei a Birnin Tehran

    .....

    Asalin hoton, Getty Images

    Dubban masu makoki ne suka taru a yankin Mosalla da ke birnin Tehran domin halartar jana'izar Ayatollah Ali Khamenei, tsohon jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

    An buɗe ƙofofin arewacin harabar Mosalla ga jama'a da safiyar Asabar, inda aka ajiye akwatin gawarsa domin mutane su yi masa bankwana na ƙarshe.

    Mahukuntan Iran sun ce an shirya zaman makoki da jana'izar na tsawon kwanaki shida, tare da hasashen cewa tsakanin mutum miliyan 15 zuwa 20 ne za su halarci bukukuwan da za a gudanar a birane daban-daban na Iran da Iraq.

    Wakilin kamfanin dillancin labaran AFP ya ce dubban mutane sun cika harabar Mosalla tun kafin isowar akwatin gawar, yayin da manyan jami'ai da wakilai daga sassa daban-daban na yankin suka halarci jana'izar.

    Ana sa ran bukukuwan za su jawo hankalin miliyoyin mutane a kwanaki masu zuwa yayin da ake ci gaba da gudanar da zaman makokin tsohon jagoran na Iran.

  11. Assalamu alaikum!

    Masu bibiyar shafin labaran kai tsaye na BBC Hausa,Barkanmu da wannan safiya ta ranar Asabar.

    Kamar kodayaushe, za mu kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Aisha Babangida ce ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokacin.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.