Ivory Coast na daf da yin bankwana da gasar kofin Afirka

Asalin hoton, Getty Images
Mai masaukin baki, Ivory Coast na daf da bankwana da gasar cin kofin Afirka, bayan da Equatorial Guinea ta ɗura mata 4-0 ranar Litinin.
Wasa na uku a rukunin farko da suka buga kenan, inda Equatorial Guinea ta haɗa maki bakwai, ita kuwa Ivory Coast maki ɗaya ne da ita.
Equatorial Guinea ta ci kwallo biyu ta hannun Emilio Nsue, sai Pablo Ganet ya ci na uku daga bugun kusurwa, sannan Yannick Buyla ya zura na huɗu a raga.
Wannan wani sakamako ne mai ban al'ajabi a tarihin babbar gasar tamaula ta Afirka.
Ivory Coast ta ci kwallo biyu ta hannun Ibrahim Sangare ana sokewa, lokacin da tuni an zura mata ɗaya a raga.
Haka kuma tawagar Ivory Coast ta ɓarar da damarmaki da yawa a wasan karshe a rukunin farko.
Ivory Coast za ta jira ko za ta samu zuwa mataki na biyu, bayan da za a ɗauki tawaga huɗu, waɗanda suka yi na uku da maki mai yawa.
Tawaga biyu ce daga kowanne rukuni za ta kai zagayen gaba kai tsaye, yayin da za a haɗa da huɗun da suka yi na uku a rukuni.











