Waiwaye: Barazanar kafa gwamnatin riƙon kwarya da zanga-zangar da aka yi wa CBN

An wallafa

Abubuwa da dama sun faru a Najeriya a wannan makon da ya gabata, waɗanda kai tsaye suka shafi rayuwar al'ummar ƙasar.

Ga wasu daga cikin muhimmai da muka rairayo muku domin tunatar da ku a kansu.

.

Asalin hoton, El-Rufa'i/BAhmed/Ganduje

Bayanan hoto, An riƙa samun kalaman da suke nuna ɓaraka kai tsaye tsakanin gwamnoni biyu da Shugaba Buhari

Gargaɗin da Buhari ya yi kan gwamnatin riƙon kwarya

Fadar shugaban ƙasar Najeriya ta ce babu ƙamshin gaskiya cikin kalaman da ake yaɗawa kan cewa Muhammadu Buhari na shirin miƙa mulki ga gwamnatin riƙon ƙwarya.

Cikin wata tattaunawa da ya yi da BBC, mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa kan lamuran yaɗa labarai Malam Garba Shehu ya ce, "ya kamata a daina ɗaukar lamarin gwamnatin riƙo da wasa, maganar zaɓe na nan daram."

Yayin da aka jiyo wasu shugabannin na zargin cewa Shugaba Buhari na neman daƙile kafafun dimokradiyyar Najeriya, a wani gefen kuma iƙirari ne kan cewa ƙarancin naira da ake fama da shi a Najeriya wani ɓangare ne na janyo koma baya ga zaɓe mai zuwa da za a gabatar nan da kwanaki, da kuma shirin miƙa iko ga gwamnatin riƙo.

A nasa martanin kakakin shugaban ƙasar ya ce wannan wani salo ne mai cike da haɗari da wasu mutane suka ɗauka waɗanda suke ganin za su iya faɗuwa zaɓen.

Zanga-zangar da aka yi wa CBN a Legas da Abuja

.

An samu ɓarkewar yamutsi a wajan ofishin babban bankin Najeriya da ke birnin Lagos sakamakon ƙarancin kuɗin da ake fuskanta a ƙasar.

Ɗaruruwan mutane waɗanda suke son su musanya tsofaffin takardun kuɗinsu da sabbin sun yi wa bankin ƙawanya.

Wasu sun yi ƙoƙarin haura wa ta katangar da ta kewaye ginin.

An samu kwatankwacin irin wannan zanga-zanga a ranar Laraba a birnin tarayyar Abuja, inda har masu son a sauya musu kuɗaɗen suka hana ma'aikatan CBN fita ta ƙofar da suka saba.

Sai dai babban bankin ya fitar da wata sanarwa in da ya musanta cewa ya bayar umurci bankunan kasuwancin suka ci gaba da karɓar tsoffafin takardun kuɗin naira 500 da 100.

Ƙarancin takardun kuɗin ya janyo ɓarkewar tarzoma a wasu sassan Najeriya a baya bayan nan.

Umarnin El-Rufa'i kan ci gaba da karɓar tsofaffin kuɗi

Nasir el-Rufai

Asalin hoton, El Rufa'i

Gwamnan Jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai ya umarci al'ummar jihar da su ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kuɗi na naira 500 da 1000 bayan da shugaba Buhari ya jaddada matsayin Babban Bankin ƙasar na soke amfani da kuɗin.

A wani jawabi da gwamnan ya yi ga al'ummar jihar a jiya Alhamis, jawabin da ke zama kamar na ƙalubalantar shugaban ƙasar, ya bayyana shirin canja kuɗin a matsayin wani makami da jiga-jigan jam'iyya mai mulki da mkusantan Shugaba Buhari suka ɓullo da shi domin dakatar da ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu nasara a zaben 25 ga watan nan na Fabrairu.

Gwamnan ya bayyana shirin a matsayin na rashin imani, wanda ya haddasa talakawan ƙasar tsananin wahala, waɗanda ya ce su ne shirin ya tagayyara.

Ya ce shugabancin Babban bankin ƙasar, CBN, ya yaudari Shugaba Buhari da cewa an ɓullo da shirin ne da nufin daƙile 'yan siyasa da suka tara maƙudan kuɗade domin sayen ƙuri'a lokacin zaɓe.

CBN ya yi amai ya lashe

CBN

Asalin hoton, cbn

Babban Bankin Najeriya ya janye batun ci gaba da karɓar takardun kuɗi na N1,000 da 500, bayan a baya ya tabbatar wa BBC cewa ya umurci bankuna su ci gaba da karɓar tsofaffin takardun kuɗin.

Tun farko, Babban Bankin na Najeriya ta bakin daraktansa na yaɗa labaru, Osita Nwanisobi ya tabbatar wa BBC cewar ya bai wa bankuna umurnin ci gaba da karɓar tsofaffin takardun kuɗi na 1,000 da kuma 500.

Sai daga baya bankin ya fitar da wata takarda ɗauke da sa hannun daraktan yaɗa labarun na CBN inda yake musanta hakan.

Bayan da BBC ta sake kiran sa domin tantance bayanin, Mr Nwanisobi ya ce bai da abin da zai fada baya ga wannan sanarwa da ya fitar daga baya.

Shirin sadaukar da hutu daga 'yan majalisar Najeriya

.

Asalin hoton, senate

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Yayin da ake ci gaba da kiki-kaka tsakanin bangaren zartarwa da wasu gwamnatocin jihohi a Najeriya game da batun sauyin kudi, 'yan majalisar dattawan kasar sun ce za su iya katse hutun da suke yi idan ta kama domin su samar wa al'ummar kasar mafita.

‘Yan majalisar dattawan sun bayyana hakan ne bayan da shugaban kasar Muhammadu Buhari, ya umarci babban bankin kasar ya fitar da tsoffin takardun naira dari biyu domin a ci gaba da hada-hada da su sakamakon karancin da ake fuskanta na sabon kudi, duk kuwa da cewa kotu ta umarci gwamnati ta saurara.

Sanata Uba Sani, shi ne shugaban kwamitin majalisar dattawan da ke kula da harkar banki, ya shaida wa BBC cewa ya kamata bangarorin gwamnati su dinga martaba juna ta yadda dimokradiyya za ta bunkasa.

Ya ce, "Kamar yadda shugaban kasa ya yi jawabi cewa yana so a ci gaba da amfani da tsohon kudi na naira 200, to a bangarenmu na majalisar dattawa muna ganin wannan mataki na da matukar hadari.”

Albishirin da Emefile ya yi wa 'yan Najeriya

Emefile

Asalin hoton, CBN

Shugaban Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefile ya ce sai nan gaba ‘yan Najeriya za su ga alfanun sauyin kudin da gwamnati ke kokarin aiwatarwa a yanzu.

Emefile ya bayyana haka ne a lokacin da ya gana da manema labaru bayan ganawa da shugaban kasar Mubammadu Buhari, a ranar Alhamis.

Al’ummar Najeriya dai na ci gaba da kokawa a kan wahalhalun da sauyin kudin ya haifar sanadiyyar karancin sababbin kudin da aka sauya wa fasali.

Ko a ranar ta alhamis, sai da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya bayar da izinin babban bankin ya saki tsofaffin takardun kudin domin ci gaba da amfani da su har zuwa ranar 10 ga watan Afrilu.

Sai dai Emefile ya ce an tsara sauya fasalin kudin ne domin cimma manyan muradu uku na gwamnatin shugaba Buhari.

Mutum shida sun mutu tara sun jikkata a haɗarin tirelar albasa da bas a Kwara

Jami'an hukumar kiyaye afkuwar hadura a Najeriya

Asalin hoton, FRSC

Mutane shida sun rasa ransu tara kuma suka jikkata a wani haɗarin mota da ya auku a Jihar Kwara, a kan titin Ganmo da ke yankin ƙaramar hukumar Ifelodun a jiya Laraba.

Bayanai sun nuna cewa haɗarin ya faru ne tsakanin wata motar bas ta haya kirar Suzuki, mai lamba BDJ-134XB da kuma wata tirela shuɗiya, ƙirar DAF mai lamba ABC435XN, wadda ta taso daga Jihar Sokoto, da albasa, kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa.

Wasu sun ce tirelar ce ta ƙwace wa direbanta saboda gudun da yake yi ta kara wa bas ɗin.

Jaridar ta ce a tattaunawar da ta yi da shugaban hukumar kiyaye haɗura ta ƙasar (FRSC), a jihar Frederick Ogidan, ya tabbatar da aukuwar haɗarin.