Chelsea ta cimma yarjejeniya da Fofana, Man Utd na son dauko Morata

An wallafa

Chelsea ta cimma yarjejeniya da dan wasan baya na Faransa mai shekara 21, Wesley Fofana game da tafiyarsa kungiyar, sai dai har sau biyu kungiyar da yake yi ma wasa, wato Leicester City na kin amincewa da tayin da Chelsea din ta yi. Inda Leicester ke bukatar Blues din su biya sama da £80m kan dan wasan. (Mail Online) 

Haka nan kuma da alama dan wasan tsakiya na Netherlands, Frenkie de Jong, da dan wasan gaba na Gabon, Pierre-Emerick Aubameyang, na kan hanyarsu ta komawa Stamford Bridge da wasa, kasancewar Chelsea din ita ce kan gaba a kokarin daukar ‘yan wasan daga Barcelona. (Express Online)

Sai dai kuma, De Jong ya fada wa abokan wasansa na Barcelona cewar da yiwuwar Manchester United zai koma. (Metro)

Amma ita Barcelona a shirye take ta fara tattaunawa da Chelsea kan Aubameyang. (Metro)

Manchester United ta tattauna da Atletico Madrid kan yiwuwar dauko dan wasan gaba na Sifaniya, Alvaro Morata, mai shekara 29, a kan kudi £30m. (The Athletic, via Mail Online)

Haka nan kuma Manchester United din ta kara jaddada wa Paris St-Germain cewar Marcus Rashford, ba na sayarwa ba ne. (Mail on Sunday)

Sai dai ita Paris St-Germain na so ne ta bai wa Marcus Rashford din kwataragi mai tsawo, domin ya rinka murza kwallo tare da matashin dan wasan gaba na Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 23. (Sunday Times - subscription required)

Dan wasan tsakiya na Tottenham da Argentina, Giovani Lo Celso, mai shekara 26, yana Sifaniya domin kammala shirye-shiryen komawa Villarreal a matsayin aro, har zuwa karshen wannan kaka. (Fabrizio Romano)

Juventus na tattaunawa da dan wasan gaba na Netherlands, Memphis Depay, mai shekara 28, wanda zai kawo karshen kwantaraginsa da Barcelona da zarar aka cimma yarjejeniya. (Fabrizio Romano) 

Matashin dan wasan baya na Anderlecht, Sergio Gomez, mai yi wa kungiyar wasan kwallon kafa ta ‘yan kasa da shekara 21 ta Sifaniya, wasa, ya isa Manchester City, yayin da ake sa ran kammala yarjejeniyar tafiyarsa kan kudi £11m. (Fabrizio Romano)

Akwai yiwuwar mai horas da Manchester City, Pep Guardiola zai so ya dauko dan wasan baya na Arsenal, Kieran Tierney, mai shekara 25, domin karfafa bayan kungiyar tasa. (Mail on Sunday) 

Dan wasan tsakiya na Faransa Tanguy Ndombele, wanda ke buga wa Tottenham wasa ya amince ya tafi Napoli a matsayin aro har karshen kakar wasa ta bana. (Fabrizio Romano, via Sun Online)

Udinese ta cire dan wasan baya Destiny Udogie, mai shekara 19, daga tawagarta yayin da yake shirin zuwa Tottenham domin gwajin lafiyarsa a ranar Talata mai zuwa. (Fabrizio Romano)

Newcastle United na tattaunawa da Benfica a kokarinta na cimma yarjejeniya domin daukar dan wasan gaba na Portugal, Goncalo Ramos, wanda farashinsa ya kai sama da £35m. (Sunday Express)