Me ya janyo musayar yawu tsakanin Rarara da Davido?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Wata cece-ku-ce ta ɓarke a shafukan sada zumunta tsakanin fitattun mawaƙan Najeriya biyu Davido da Rarara.

A ranar Talata da daddare ne dai fitaccen mawaƙin siyasa a arewacin Najeriya, Dauda Kahutu Rarara ya wallafa wani bidiyo a shafukansa na sada zumunta, inda a ciki ya soki fitaccen mawaƙin Kudancin ƙasar David Adedeji Adeleke da aka fi sani da Davido.

Davido dai ya bayyana ne a wani bidiyon waƙa da ya gudanar a bikin shirye-shiryen fara gasar Kofin Duniya, sanye da riga mai ɗauke da tutar Najeriya rubuce da sunayen yara ɗaliban da aka sace a jihar Oyo.

A watan da ya gabata ne dai wasu mahara masu iƙirarin jihadi suka kai hari makarantar yara a jihar Oyo tare da sace ɗalibai da wasu malamansu, lamarin da ya tayar ƙura da ke ci gaba da janyo wa gwamnatin Najeriya suka daga ƴan ƙasar.

Me ya haɗa su?

Bayyanar da Davido ya yi sanye da rigar da ke ɗauke da sunayen yaran da aka sace a jihar Oyo a bikin shirye-shiryen fara gasar Kofin Duniya, ya ce ya yi ne domin nuna goyon baya ko tausayawa ga ɗaliban.

Sai dai a nasa ɓangare, Rarara na ganin matakin na Davido tamkar kunce wa gwamnatin Bola Tinubu - da yake goyon baya - zane ne a kasuwa.

Ba dai wannan ne karon farko da ake samun taƙun saƙa tsakanin fitattun mawaƙan Najeriya ba, lamarin da wasu masana ke alaƙantawa da 'hassadar mawaƙa'.

Abin da Rarara ya faɗa

Cikin bidiyon nasa da ya yi wa take da martani, mai tsawon minti 11, Rarara ya yi magana kan batutuwa masu yawa, sai dai ya fara ne da batun na Davido.

Ya bayyana matakin na Davido a matsayin ''nuna goyon bayan ƙungiyar Ansaru'' ta masu iƙirarin jihadi, waɗanda ake zargi da sace ɗaliban na jihar Oyo.

''Ta yaya za ka ɗauki sirrin Najeriya na cikin gida, ka kai shi fagen duniya'', in ji shi.

Rarara ya zargi Davido da siyasansar da matsalar tsaro, bayan da ya yi zargin cewa ƙanin mahaifin Davido na takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar Accord Party.

Rarara ya ce batun tsaro abu ne da bai kamata a yi masa karan-tsaye ba.

''Ya kamata ka buƙaci a yi maka bayanin ina aka tsaya, da matakin da ake kai yanzu kafin ka yi magana a kai'', a cewar mawaƙin siyasar.

Rarara ya yi ikirarin cewa mayaƙan Ansaru sun sace ɗaliban Oyo ne da nufin a sako muku manyan shugabanninsu da aka sace.

''Sun ce ba za su saki yaran ba, har sai an sakar musu jagororinsu, amma shugaban ƙasa da shugabannin tsaro suka ce ba za a saki shugabannin ƙungiyar ba, kuma kuma suke ƙoƙarin ƙwato daliban'', kamar yadda ya yi iƙirari.

Mawaƙin ya kuma zargi wasu ƴansiyasa da amfani da matasa masu amfani da shafukan sada zumunta wajen yayata batun matsalar tsaro.

Martanin Davido ga Rarara

A nasa ɓangare, mawaƙi Davido ya yi martani ga kalaman na Rarara a shafinsa na X.

A martanin nasa ya yanko bidiyon na Rarara daidai wurin da ya yi magana a kansa ya kuma sake wallafawa tare da yi wa Rarara shaguɓe.

A shaguɓen nasa bai yi dogon rubutu ba, abin da kawai ya rubuta shi ne ''Debidooo'' tare da saka alamar kuka a gaba, kodayake bai yi ƙarin haske ba, amma mutane na ganin cewa yana so ne ya nuna Rarara bai ma iya faɗar sunansa ba.

Wato maimakon Davido, yana ganin Rarara ''Debidooo'' yake cewa.

Sai ba da jimawa ba da wallafa saƙon na Davido sai Rarara ya mayar masa da martani da cewa ''ka shiga taitayinka Davido''.

Nan take kuma Davidon ya sake mayar masa da martani da Hausa da a ciki yake cewa ba zai mayar wa Rarara martani ba, saboda a cewarsa ba shi da ilimi.

Ya kuma sake wallafa wani saƙon da a ciki yake cewa duk wanda yake da kishin Najeriya ba zai yi shiru kan matsalar tsaron da ƙasar ke ciki ba.

Abin da jama'a ke cewa

Tun bayan da wannan cece-kuce ta kaure mutane a shafukan sada zumunta sun ci gaba da tafka muhawara a shafukan.

Inda suke goyon bayan mawaƙin da suke so, tare da sukar ɗayan.

Wani mai suna Emeritus ya goyi bayan iƙirarin na Rarara inda ya ce:

''Davido ka fita daga sabgar siyasa, siyasa ba taka ba ce, siyasa ta mutanen da ba na kirki ba, za ka zubar da kimarka'', kamar yadda ya yi tsokaci a ƙasan saƙon da Davido ya wallafa.

Amma wata mai amfani da shafin X da ke goyon bayan Davido mai suna Prisca Ezenyinwa ta soki Rarara da rashin sukar satar ɗaliban.

''Za su yi kuka da yawa, ka yi abin da ya dace, su ba sa son duniya ta san abin da ke faruwa a Najeriya''.

''Bai soki satar yaran ba da kuma kashe ɗaya daga cikin malamnasu, amma ya saka kamera yana kiran Debidoo'', kamar yadda ta yi martani.

Wane ne Rarara?

An haifi Dauda Adamu Kahutu Rarara wanda aka fi sani da Rarara, a garin Kahutu da ke jihar Katsina. Sai dai kuma shahararren mawaƙin siyasar yana zaune a jihar Kano.

Mawaki ne da ya shahara a waƙoƙin ƴan siyasa. Rarara ya taka muhimmiyar rawa wajen rera waƙoƙin ga ƴan jam'iyyar APC a babban zaɓen Najeriya na shekarar 2015, musamman ma ga tsohon shugaban ƙasar, marigayi Muhammadu Buhari da gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari.

Za a iya cewa waƙar da a baya-bayan na da Rarara ya yi wadda ta fi shahara a arewaci da kudanci ƙasar ita ce waƙar "Omologo" wadda ya rera wa shugaban Najeriya, Bola Ahmad Tinubu.

Wane ne Davido?

David Adedeji Adeleke, da aka fi sani da Davido mawaƙi ne ɗan Najeriya wanda amon waƙoƙinsa ke amo a Afirka da ma duniya.

Matashin mawakin mai shekaru 34 an haife shi ne a Atlanta da ke Georgia amma ya tashi a birnin Legas, ya fara suna ne a shekarar 2011 sakamakon waƙarsa mai suna "Dami Duro".

Ana yi masa kallon wani mawaƙi da ya sauya fasalin waƙoƙin ƴan asalin Afirka a idanun duniya.

Davido na ɗaya daga cikin mawaƙan duniya da suka cashe a filayen wasanni a lokacin buɗe gasar Kofin Duniya ta 2026, a birnin Los Angeles na Amurka.