Brentford ta kara yaga barakar Man United

An wallafa

Manchester United ta sha kashi da ci 4-0 a gidan Brentford a wasan mako na biyu a gasar Premier League ranar Asabar.

Brentford ta fara cin kwallo a minti na 10 da take leda ta hannun Pelenda Joshua Da silva, minti takwas tsakani Mathias Jensen ya zura na biyu a raga.

A minti na 30 Ben Mee ya ci wa Brentford kwallo na uku, sannan Bryan Mbeumo ya kara na hudu saura minti 10 su je hutu.

Erik Ten Hag ya zama na biyu a matakin sabon koci da ya yi rashin nasara a wasan farko a waje a Manchester United.

Wanda ya yi wannan rashin kokarin shi ne Sir Alex Ferguson a Nuwambar 1982 a lokacin da Oxford ta ci United 2-0.

Ten Hag, wanda ya fara jan ragamar kungiyar Old Trafford a bana, ya sha kashi a wasa biyu kenan a jere.

'Yan wasan Brentford 11 da suka fuskanci United

Rabon da United ta yi rashin nasara a hannun Brentford shi ne 2-0 a zagaye na biyar a FA Cup a Fabrairun 1938.

Tun kan wasan na ranar Asabar, Brentford ta samu maki daya kacal daga fafatawa shida a kan United, tun bayan gida da waje da ta yi 1936/37.

Karo na biyu a jere kenan da aka doke United a kakar nan, bayan da Brighton ta yi nasara da ci 2-1 a Old Trafford a karawar makon farko.

Brentford ta zama ta uku da ta ci United kwallo hudu tun kan hutu a Premier League, bayan Tottenham a Oktoban 2020 da Liverpool a Oktoban 2021.

'Yan wasan United 11 da ta fara karawa da Brentford da su

Ranar 22 ga watan Agusta, United za ta karbi bakuncin Liverpool a Old Trafford a wasan mako na uku a gasar Premier League ta bana.

Liverpool wadda ta tashi 2-2 a gidan Fulham a wasan makon farko, za ta karbi bakuncin Crystal Palace ranar Litinin 15 ga watan Agusta.

Ita kuwa Brentford wadda ta ttashi 2-2 a gidan Leicester City a karawar makon farko, za ta ziyarci Fulham ranar 20 ga watan Agusta, domin buga wasan mako na uku a babbar gasar tamaula ta Ingila ta bana.