Man Utd ta fara neman Ziyech, an yi wa Barca tayin Bellerin

An wallafa

Manchester United na son ta dauko dan wasan gefe na Chelsea, Hakim Ziyech, mai shekara 29, bayan da ta gaza hana tafiyar Timo Werner daga Chelsea zuwa RB Leipzig. (Manchester Evening News)

Da yiwuwar Newcastle United za ta nemi sayen dan wasan Chelsea da Amurka Christian Pulisic, mai shekara 23. (The Athletic, via Mail)

Dole sai Chelsea ta yi da gaske idan tana son dakile Juventus daga sayen dan wasan tsakiya na Italiya, Jorginho, mai shekara 30, matukar Juve ta sayar da dan wasanta na tsakiya dan asalin Faransa, Adrien Rabiot, mai shekara 27 ga  Manchester United. (Express)

West Ham ta yi wa Barcelona tayi mai tsoka domin sayen dan wasan gaba na kungiyar, dan asalin Netherlands, Memphis Depay mai shekara 28. (Football Insider)

Bordeaux ta amince da tayin kudi yuro miliyan 4 (£3.4m) daga Nottingham Forest domin sayar mata da dan wasan gaba Hwang Ui-jo, mai shekara 29, dan asalin kasar Koriya ta kudu. (L'Equipe - in French)

Napoli ta cimma yarjejeniya da Tottenham domin daukar dan wasan tsakiya na Faransa Tanguy Ndombele, mai shekara 25, a matsayin aro, sannan kuma tana da damar sayen sa daga baya. (Fabrizio Romano)

Ana gab da kammala yarjejeniyar tafiyar Willian zuwa Fulham, bayan da dan wasan dan asalin Brazil, mai shekara 34 ya soke kwantaraginsa na wasa a kungiyar Corinthians. (Nicola Schira)

Ita ma Fulham ta shiga cinikin dan wasan gaba na Senegal, Bamba Dieng, mai shekara 22, daga Marseille, yayin da ita ma Celtic ke ta kokarin ganin ta dauki dan wasan. (90min)

An yi wa Barcelona tayin dan wasan baya na Sifaniya Hector Bellerin, yayin da dan wasan mai shekara 27 ya kawo karshen kwantaraginsa da Arsenal. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Barca na tattaunawa da Manchester United kan batun sayar da dan wasanta na baya, dan asalin kasar Amurka Sergino Dest, mai shekara 21, inda Barca din ke bukatar United ta biya yuro miliyan 20 (£16.9m). (Sport, via Bild)

Bugu da kari United din na ci gaba da neman mai tsaron raga da zai rinka taimaka wa David de Gea, inda take sanya ido kan tsohon golan Ingila na kungiyar Southampton, Alex McCarthy, mai shekara 32. (90min)

Ander Herrera ya amince ya sake komawa Athletic Bilbao, inda tsohon dan wasan na Sifaniya mai shekara 32 ya baro lokacin da ya tafi Manchester United a shekarar 2014. Hakan na iya faruwa ne matukar ya cimma yarjejeniya da Paris St-Germain game da kudinsa na wa’adin kwantaraginsa da ta rage. (L'Equipe - in French)

West Ham ta yi rashin nasara a tayin da ta yi wa Sporting Lisbon na kudi £25m a kokarinta na sayen Matheus Nunes mai shekara 23, bayan da dan wasan tsakiyar na Portugal ya bayyana karara cewar baya son zuwa kungiyar. (Mail)

Mai horas da Manchester City Pep Guardiola na sa ran cewa Sergio Gomez zai zama dan wasa na karshe da kungiyar za ta dauka a wannan lokaci na musayar ‘yan wasa, yayin da dan wasan bayan, dan asalin Faransa mai shekara 21 ke gab da sanya hannu kan yarjejeniyar da kudinta ya kusa yuro 10m (£8.5m) daga Anderlecht. (Guardian)

Mai horas da kungiyar Wolves Bruno Lage na ta kokarin ganin an rinka biyan dan wasan tsakiya na Portugal Ruben Neves, mai shekara 25, albashin £100,000 a mako, bayan da kungiyoyin Manchester United da Arsenal suka fara nuna kwadayinsu kan dan wasan. (Sun)