Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Spurs na harin Wharton, Liverpool ta dage kan Diomande
Tottehnham ta sahun sauran ƙungiyoyi da ke sonsiyen ɗan wasan Crystal Palace da Ingila Adam Warton. (Teamtalk)
RB Liepzig ta ƙi amincewa da tayin fam miliyan 87 da Liverpool ta yi na siyar mata da Yan Diomande, inda su kuma Liverpool ke neman fam miliyan 113 akansa. (Liverpool Echo)
Fulham sun yi watsi da tayin fam miliyan 17 da ƙungiyar Tarbzonspor ta yi don ganin ta siyar mata da ɗan wasa bayan Najeriya, Chibuike Nwaiwu. (Fotomac - in Turkish)
Totthenham ba su da wani shiri na siyar da Mason Greenwood, yayin da Roma ke da ƙudin siyen ɗan wasan ƙasa da farashin da Marseille ke nema kan ɗan wasan. (Mail)
Everton, Tottenham da Ipswich na kokawar ganin sun siye ɗan wasan Kamaru Karl Etta Eyong daga Levante a wannan kaka. (Teamtalk)
Celtic sun ƙi amince da tayin fam miliyan 25 da Nottingham Forest suka yi, kan ɗan wasan tsakiyar ta Arne Engels, sai dai ƙofar su a buɗe ta ke ga tayin ɗan wasan, a dai-dai lokacin da Crystal Palace da Borussia Dortmund suma ke son ɗaukarsa. (Football Insider)
Leeds na harin ɗan wasan Norther Ireland Shea Charles daga Southhampton a wannan kaka, inda ake sa ran siyar da ɗan wasan kan fam miliyan 20. (Mail)
Haka kuma Leeds ɗin dai na son siyen ɗan wasan Jamus Julian Brandt, da ke barin Borussia Dortmund a wannan kaka. (Yorkshire Evening Post)
Wolves ta ƙagu su ɗauko ɗan wasan Scotland Che Adams, daga Torino da ke Italiya a wannan kaka. (Tuttomercato - in Italian)