Chelsea ta amince da tayin da Aston Villa ta yi wa Maatsen

Ian Maatsen.

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Aston Villa ta kulla yarjejeniya da Chelsea, domin daukar mai tsaron bayan tawagar Netherlands Ian Maatsen kan fara kakar bana.

Mai shekara 22, farashinsa ya kai daga £35m zuwa £40m, idan aka hada da tsarabe-tsarabe, idan aka kammala auna koshin lafiyarsa.

Ana sa ran mai tsaron bayan zai koma Villa Park da taka leda kan kwantiragin kaka shida.

Maatsen ya amince da tayin da Villa ta yi masa, saboda kungiyar za ta buga Champions League a kakar badi, bayan da ya kai wasan karshe a Borussia Dortmund a gasar ta zakarun Turai da ya buga wasannin aro.

Tuni dai Chelsea ke tattaunawa kan daukar dan wasan Villa, Jhon Duran daga cikin yarjejeniyar da suka kulla ta musaya da Maatsen.

A farkon watan nan Dortmund ta yi kokarin sayen Maatsen, sakamakon rawar da ya taka a wasannin aron da ya yi mata, amma ta kasa biyan £35m da ake bukata.

Cikin watan Janairu, Maatsen ya saka hannu kan kwantiragin wata 12, domin ci gaba da zama dan kwallon kungiyar da ke Stamford Bridge.

Yanzu haka yana tare da tawagar Netherlands a Jamus a gasar Euro 2024, wanda zai je Villa Park a auna koshin lafiyarsa bayan gasar nahiyar Turai.

Chelsea ta dauki Maatsen daga PSV Eindhoven a 2019 daga lokacin ta bayar da aronsa ga Charlton da Coventry da Burnley, sannan ta tura shi Dortmund karkashin jagorancin Mauricio Pochettino.

Zai bar Stamford Bridge bayan da ya buga mata karawa 16.