Atletico ta ci Man City a wasan karshe na sada zumunta a Asia

Asalin hoton, Getty Images
Manchester City ta yi rashin nasara a hannun Atletico Madrid da ci 2-1 a wasan sada zumunta da ta buga na karshe a Asia, don tunkarar kakar bana.
Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Atletico ta fara cin kwallo ta hannun Memphis Depay da kuma Yannick Carrasco.
Daga baya ne City ta zare ɗaya ta hannun Ruben Dias, saura minti huɗu a tashi daga karawar.
Tun farko an yi lattin take leda, sakamakon zubar ruwan sama kamar da bakin kwarya a karawar ta birnin Seoul.
Kyle Walker, wanda ake alakanta shi da komawa Bayern Munich kafin fara kakar bana, ya buga tamaula ta bugi turke a wasan.
Haka kuma ya rage kaɗan 'yan wasan City da suka haɗa da Erling Haaland da Phil Foden kaɗan su zura kwallo a raga tun kan hutu.
City mai rike da Premier League da FA Cup da Champions League za ta fuskanci Arsenal a Wembley a Community Shield ranar 6 ga watan Agusta.






