Chelsea ta huce haushi a kan Wolves

Asalin hoton, Getty Images
Chelsea ta huce haushi a kan Wolverhampton a Premier League, inda ta je ta ci 6-2 a wasan mako na biyu ranar Lahadi a Molineux.
Wolves, wadda ta yi rashin nasara a wasan makon farko a Arsenal, ta ci ƙwallayenta ta hannun Matheus Cunha da Jorgen Strand Larsen.
Noni Madueke ne ya ci wa Chelsea uku rigis a raga a minti na 49 da 58 da kuma 63, yayin da Nicolas Jackson da Cole Palmer da Joao Felix kowanne ya ci ɗaya.
Kenan Madueke ya zama na 23 da ya ci wa Chelsea ƙwallo uku rigis a Premier League a tarihi.
Shi kuwa Enzo Maresca ya zama koci na farko a wasansa na farko a Premier League a waje da ya ja ragamar ƙungiyar da ta zura ƙwallo shida a karawa.
Maresca ya karɓi aikin horar da ƙungiyar Stamford Bridge, bayan da aka kammala gasar Premier da ta wuce, inda ya maye gurbin Mauricio Pochettino.
Maresca ya koma Chelsea daga Leicester City, bayan da ya ja ragamar ƙungiyar ta lashe Championship a bara da samun gurbin shiga Premier League.
Felix ya sake dawowa Chelsea a karo na biyu daga Atletico Madrid, inda Chelsea ta bayar da Conor Gallagher.
A kakar da ta wuce Wolves ta ci Chelsea gida da waje, inda ta yi nasara 2-1 a Molineux ranar 24 ga watan Disamba da cin 4-2 a Stamford Bridge ranar 4 ga watan Fabrairu
Chelsea ta fara da rashin nasara a wasan makon farko a babbar gasar tamaula ta Ingila ta 2023/24, inda ta yi rashin nasara 2-0 a hannun Manchester City a Stamford Bridge.
Ranar Alhamis, Chelsea za ta je Servette, domin buga wasa na biyu na neman gurbin shiga Europa Conference League na bana, an doke Servette 2-0 a Stamford Bridge a wasan farko a makon jiya.
Daga nan Chelsea za ta karbi bakuncin Crystal Palace a wasan mako na uku a Premier League ranar Lahadi 1 ga watan Satumba.
Ita kuwa Wolves za ta karɓi bakuncin Burnley ranar Laraba 28 ga watan Agusta a League Cup, sannan ta je Nottingham Forest ranar Asabar 31 ga watan Agusta a wasan mako na uku a babbar gasar tamaula ta Ingila.










