Eriksen zai buga wa Denmark Gasar Cin Kofin Duniya a Qatar

Christian Eriksen

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

An bayyana Christian Eriksen cikin 'yan kwallon Denmark na kwarya-kwarya, kafin ta tace wadanda za su buga mata kofin duniya a Qatar.

Za a fara gasar cin kofin duniya tsakanin 20 ga watan Nuwamba zuwa 18 ga watan Disambar 2022.

Eriksen mai taka leda a Manchester United, mai shekara 30 ya fadi a cikin fili ana tsaka da wasa a Euro 2020 da Finland.

Daga baya likitoci suka yi masa aiki, sannan suka saka masa wata na'urar da take taimaka masa yin numfashi yadda ya kamata.

Hakan ne ya sa ya bar Inter Milan, bayan da dokar Serie A ba ta amince dan kwallo ya taka leda mai dauke da na'urar da za take taimaka masa ba a jikinsa.

Denmark za ta fara wasa da Tunisia ranar 22 ga watan Nuwamba.

Dole tawaga ta gabatar da 'yan wasan da za su buga mata gasar kofin duniya ga Fifa ranar 13 ga watan Nuwamba.

Eriksen ya koma taka leda a Brentford kan kwantiragin wata shida, bayan da Inter ta soke yarjejeniyar da take tsakaninsu.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Tohon dan kwallon Tottenham ya koma Manchester United da murza leda a bana, bayan da wa'adinsa ya kare a Brentford.

Idan Denmark ta kara da Tunisia za ta buga wasan gaba da mai rike da kofin Faransa ranar 26 ga watan Nuwamba, sannan da Australia ranar 30 ga watan Nuwamba a rukuni na hudu.

'Yan wasa na kwarya-kwarya da Denmark ta sanar:

Masu tsaron raga: Kasper Schmeichel (Nice), Oliver Christensen (Hertha Berlin).

Masu tsaron baya: Simon Kjaer (AC Milan), Joachim Andersen (Crystal Palace), Joakim Maehle (Atalanta), Andreas Christensen (Barcelona), Rasmus Kristensen (Leeds United), Jens Stryger Larsen (Trabzonspor), Victor Nelsson (Galatasaray), Daniel Wass (Brondby).

Masu buga tsakiya Thomas Delaney (Sevilla), Mathias Jensen (Brentford), Christian Eriksen (Manchester United), Pierre-Emile Hojbjerg (Tottenham).

Masu cin kwallaye: Andreas Skov Olsen (Club Bruges), Jesper Lindstrom (Eintracht Frankfurt), Andreas Cornelius (Copenhagen), Martin Braithwaite (Espanyol), Kasper Dolberg (Sevilla), Mikkel Damsgaard (Brentford), Jonas Wind (VfL Wolfsburg).