Liverpool ta lashe Community Shield bayan cin Man City

Asalin hoton, Getty Images
Sabon dan wasan da Liverpool ta Sayo, Darwin Nunez, shi ne ya ci mata kwallo na uku kuma na karshe da ya ba ta nasara kan Manchester City a Community Shield.
Man City ta sha gaban Liverpool wajen lashe kofin Premier League a kakar da aka kammala, sai dai Liverpool din ce ta samu nasara kan City a wasan da aka buga a filin King Power na Leicester City.
Dan wasan baya na Liverpool, Alexander-Arnold ne ya fara cin kwallon farko bayan dadata a cikin yadi na 18 wadda kuma ta taba Nathan Ake kafin ta shiga raga.
Sai dai sabon dan wasan Man City, Julian Alvarez, ya farke kwallon da Liverpol ta ci bayan kwallon da Phil Foden ya buga ta dawo kafarsa, inda bai yi wata-wata ba ya zira ta a raga.
Amma Mohammed Salah ya sake saka Liverpool a gaba bayan ya ci daga bugun fenariti saura minti takwas a tashi wasan bayan kwallo ta taba hannun Ruben Dias cikin yadi na 18.
Daga bisani Darmian Nunez ya ci kwallo ta uku, inda ya je gaban magoya bayan kungiyarsa yana murna.
Sabon dan wasan da City ta sayo Erling Haaland ya nuna cewa za a dama da shi a sabuwar kaka duk da cewa bai ci wa City kwallo ba, amma ya kusa ya sha kwallo bayan da ta bugi turke.
Tun da farko an tsara buga wasan ne a filin Wembley, amma aka dage zuwa filin King Power saboda wasan karshe na gasar nahiyar Turai ta mata da za a buga a ranar Lahadi.









