Partey zai ci gaba da taka leda a Arsenal - Arteta

Thomas Partey

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Kociyan Arsenal, Mikel Arteta ya ce yana sa ran Thomas Partey zai ci gaba da taka leda a kungiyar duk da rashin tabbas kan makomar dan kwallon.

Dan wasan tawagar Ghana, shi ne na baya-baya da ya halarcin sansanin Gunners a Amurka, inda take wasannin atisayen tunkarar kakar bana.

Partey, mai shekara 30, daya ne daga fitattun 'yan wasan da Al Ahli ke son dauka, domin buga babbar gasar tamaula ta Saudi Arabia.

Arsenal na niyar barin dan wasan ya je inda yake bukata, bayan da ta dauki Declan Rice kan fam miliyan 100 daga West Ham.

Partey ya koma Arsenal daga Atletico Madrid a 2020, bayan da Gunners ta biya kunshin kwantiraginsa ta fam miliyan 45.3.

Ya buga wa Arsenal karawa 33 a kakar Premier League da ta wuce da cin kwallo uku.

Arsenal ta kare a mataki na biyu a teburin Premier League da Manchester City ta lashe kofin na uku a jere na biyar a kaka shida.