Ancelotti na son ci gaba da kocin Real duk da alakanta shi da Brazil

Asalin hoton, Getty Images
Carlo Ancelotti ya ce yana son ci gaba da aiki a Real Madrid, duk da alakanta shi da aiki da kociyan Brazil.
Sai dai dan kasar Italiya tsohon wanda ya horar da Everton ya ce bai san makomar sa ba kawo yanzu.
Wasu rahotanni na alakanta Ancelotti da aikin horar da tawagar Brazil tun bayan da Tite ya yi ritaya, bayan gasar kofin duniya da aka yi a Qatar a 2022.
Wasu 'yan wasan Brazil ma sun bayyana ra'ayinsu kan dacewar Ancelotti ya ja ragamar tawagar kasar.
Shugaban hukumar kwallon kafar Brazil, Ednaldo Rodrigues ya tabbatar da cewar suna fatan daukar tsohon kociyan Chelsea da Paris Saint-Germain nan gaba kadan.
Da yake amsa tambayoyin 'yan jarida ranar Asabar kan wasan da Real za ta yi da Valladolid ranar Lahadi a La Liga, kociyan ya ce ba abin da ke gabansa illa aikin horar da kungiyar Santiago Bernabeu.
Mai shekara 63 yana da kunshin kwantiragin da zai kare da Real Madrid a karshen kakar 2024.
Koda yake kociyan na fuskantar matsi, bayan da Barcelona ta doke Real Madrid a bana karo uku, duk da ya lashe LaLiga da Supercopa de Espana da Champions League a bara.
Real ta yi nasara a kan Barcelona a La Liga, amma Barca ta dauki Sifanish Super Cup a kan Real a Saudi Arabia ta kuma doke ta a La Liga da Copa del Rey.
Wasa daya za su kara fafatawa a bana a Camp Nou a Copa del Rey daf da karshe, bayan da Barca ta je Bernabeu ta yi nasara da cin 1-0.
Ancelotti ya ce dukkan jita-jitar da ake kan makomarsa da wasu 'yan wasan, ba zai dauke hankalin kungiyar kan shirye shiryen da take na lashe Copa del Rey da Champions League da lik ba.
Barcelona ce ta daya a kan teburin La Liga da tazarar maki 12 tsakaninta da Real Madrid ta biyu.










