Liverpool na son Wharton amma za ta iya rasa Elliott, Aston Villa na son rike Disasi

Asalin hoton, Getty Images
Liverpool ta bi sahun Real Madrid da Barcelona kan dan wasan tsakiya na Ingila mai taka leda a Crystal Palace Adam Wharton, 21, kan kudi fam miliyan 60. (Daily Mail - subscription required)
Watakil Liverpool din ta dauko mai kai hari na Faransa da ke taka leda a Nkunku, 27, a kaka mai zuwa. (Footmercato - in French)
Wolves na ci gaba da zage damtse domin dauko dan wasan tsakiya na Ingila mai taka leda a Liverpool, Harvey Elliott, 22. (GiveMesport)
Kungiyoyi uku na Premier League wato Chelsea, Manchester City da Arsenal, sun yi nisa a tattaunawa da eja din dan wasan tsakiya na Brazil mai taka leda Real Madrid, Rodrygo mai shekara 24, wanda Bernabeu ke zawarci. (Fichajes - in Spanish)
Aston Villa na fatan juya zaman aron da Axel Disasi a Chelsea zuwa dindindin a kakar wasa, inda kungiyar ta fara tattaunawa da dan wasan na Faransa mai shekara 27. (Footmercato - in French)
Har wayau Chelsea, ta fitar da jerin 'yan wasan baya da ta ke son daukowa, ciki har da dan wasan Ingila meanwhile, Jarrad Branthwaite mai shekara 21, wanda ke taka leda a Everton, sai kuma na Ingila Marc Guehi, 24, da ke Crystal Palace. (Sky Sports)
Aston Villa ka iya sayo dan wasan Sifaniya Ferran Torres mai shekara 25, da ke taka leda a Barcelona, zuwa kulub dinPremier League kan kudi fam miliyan 4, idan an bude kasuwar saye da saida 'yan wasa a kaka mai zuwa. (Birmingham Mail)
Southampton na son dan wasan baya na Sturm Graz Max Johnston, 21, kan kudi fam miliyan 3. (Sky Sports)
Wrexham na duba yiwuwar dauko dan wasan tsakiya na Nottingham Forest, Lewis O'Brien mai shekara 26- wanda a yanzu ya ke zaman aro a Swansea City - bayan likkafarsu ta daga a Championship. (Football League World)









