Me ke haifar da koma baya a harkar ilimin yara a Najeriya?

Wani sabon rahotan hukumar raya Ilmi da kimiyya da kuma al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya, UNESCO, ya ce yankin Afrika na kudu da hamadar Sahara shi ne yanki ɗaya tilo a duniya da yawan yara da matasan da ba sa zuwa makaranta ke karuwa.
Asusun ya ce, akwai yara da matasa kimanin miliyan casa’in da takwas (98) da ba sa zuwa makaranta a yankin, inda Najeriya ke da miliyan ashirin, kuma shi ne adadi mafi girma a duniya.
Rahoton na zuwa ne duk da irin matakan da mahukunta musamman a Najeriya ke ikirarin cewa suna dauka a ko da yaushe wajen sake inganta ilimi a kowanne kusurwa na kasar.
Amma masana a kan harkokin ilimi a Najeriyar na ganin kuɗaɗen da ake ware wa fanni da za a yi amfani da shi wajen zamanantar da ilimin maimakon yawan gine-gine da aka fi bai wa fifiko to da an samu gagarumin ci gaba.
'Abin da ke hana yara zuwa makaranta a Najeriya'
Kwamishinan ilimi jihar Bauchi, kuma mai sharhi kan ilimin, Dr Aliyu Tilde a tattaunawarsa da BBC ya ce babban dalilin da ke hana yara zuwa makaranta a Najeriya shi ne batun nisa.
Ya ce akasari kashi 8 cikin 10 na yara da ke zuwa makaranta su na sha wahala wajen takawa ko tafiya mai nisa kafin su isa makaranta.
Ya ce wannan yanayi kuma ana samunsa a kusan kowanne bangare ko mataki na karatu kama daga firamare har zuwa sakandare da jami’a.
Sannan ya ce akwai batun talauci da ke taka rawa wajen samar da ilimi, saboda tsarabe-tsaraben ilimi na bukatar kudi, don haka idan talauci na karuwa dole a samu yawan yara da ba sa iya tafiya neman ilimi.
“Akwai kudi a fanin ilimi, sai dai yada ake kashe dukiyar ko sarrafasu na sake nakasu ko karye fannin ilimi.''
'Ana ɓarnatar da kuɗaɗe ta hanyoyi marasa tasiri'
Dr Tilde, ya ce a galibin kotun ana kashe kudi ne a fanin gine-gine, maimakon a bada fifiko wajen inganta rayuwar malamai, sayan kayan aiki da sauran abubuwan gudanar da ilimi da fuskar zamani domin samu sauki.
Sannan ya soki yada ake kashe makudan kuɗaɗe wajen sayan motocin alfarma da jindadi tsakanin ma’aikatun gwamnatoci, kudin da acewarsa zai inganta rayuwar dalibai da dama.
“Akwai shirye-shirye da yawa da za a iya amfani da su wajen karfafa gwiwar iyaye su tura yayansu makaranta”.
Ya bada misali da jihar Bauchi, da sauyin da suka kawo wajen ba su nasara har aka samu dalibai da dama da suka samu nasara a jarrabawa kammala sakandare ta WAEC.
Sannan ya soki batun ciyarwa a makarantu, yana cewa ba ya taimakawa, saboda a galibin lokutan yara mai abinci kawai suke bi ba wai karatu ba.
Sharhi
Masana dai na ganin akwai bukatar gwamnatoci su sake ɗaura damara muddin sun shirya inganta samar da ilimin Boko a Najeriya, musamman a wannan lokacin da ake samun karuwar matsaloli na barazanar da ke durkusar da kokarin samar da ilimin.
Matsalar tsaro da yajin aikin malaman jami’o’i da kuma batun rashin albashi ko inganta malamai na daga cikin abubuwan da a wannan lokaci ke tarnaki wajen samar da ilimi a Najeriya.










