Ku San Malamanku tare da Gwani Muhammadul Hadi, maja baki a fadar Sarkin Kano

Bayanan bidiyo, Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon:
An wallafa

Shirin Ku San Malamanku na wannan makon ya tattauna da Gwani Muhammadul Hadi, mai jan baki a karatun da ake yi a gidan Sarkin Kano da ke arewacin Najeriya.

Malamin, wanda yake zaune a birnin na Kano, ya fara da bayyana mana nasabarsa.

 

Asali

Ya ce: "Sunana Muhammadul Hadi, dan gwani Dahiru dan gwani Abdussamad dan gwani Mammadu dan Ali Mufri Umar, dan gwani Muhammadu dan gwami Aminamin Guruma dan gwani Girema Konduna a jihar Borno."

Malamin ya ce daya daga cikin kakanninsa, Gwani Girema, ne ya yi hijira daga Borno zuwa garin Gwauron Maje a kasar Dambatta da ke Kano.

Daga nan iyalansa suka yi arewa zuwa har kasar Damagaram a Jamhuriyar Nijar.

Gwani Hadi ya ce ya fara karatun addini ne a wajen mahaifinsa tare da sauran ‘yan uwansa, yana mai cewa "a nan muka koyi farfaru da hajjatu, kuma mun samu kulawa sosai ta fuskar koyon karatu."

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ya kara da cewa mahaifins ya yi kokari sosai wajen ganin sun samu karatu mai zurfi.

Malamin ya ce malamansa sun hadar da Muhammadul Aminu Zariya, da Malam Adumu Tasawa Nijar, da Malam Yusuf, da Malam Yusuf Limamin Jalli ,

Farin ciki

Gwani Muhammadul Hadi ya ce abin da ya fi faranta masa rai shi ne ya ji yana karanta AlKur’ani mai girma, tare da sauraron tafsirin marigayi Malam Nasiru Kabara da mahaifinsa, Gwani Dahiru da ke ja masa baki.

Tabarbarewar tarbiyya

"Babban abin da yake bata mini rai shi ne yadda zamani ya lalace ta fuskar tabarbarewar tarbiyya tare da kekashewar zukatan yaran yanzu da rashin kunya da fitsara, musammam yadda yanzu ake yi a bukuwan zamani inda ake kiran uwar Amarya da uwar Ango a je a taru a yi abin da ba shi ya kamata ba," in ji Malamin

Shawararsa ga matasa

Malamin ya ce babbar shawarar da zai bai wa matasan ita ce su yi kokari su karanci AlKur’ani musamman yadda yanzu ake samun yawaitar makaranta da mahaddata, saboda yaran yanzu kwakwalensu a bude suke ba kamar a baya ba, ya kuma gargadesu da su yi riko da koyarwar addini, su kuma guje wa abin ki wato munkari.

Abincin da ya fi  so

Malamin ya ce abincin da ya fi so shi ne Burabusko da tuwo saboda a cewarsa shi Babarbare ne.

 

'Surar da na fi jin dadin karantawa'

Suratul Kahfi da suratul Maryam su ne surorin da malamin ya ce ya fi jin dadin karanta su saboda yadda Allah ya yabi Annabawa a cikin wadannan surorin.

 

Iyali da buri

Malamin ya ce yana da mata biyu, sannan ya haifi ‘ya’ya 30 maza da mata, amma bakwai sun mutu, 23 kuma suna nan a raye.

Malamin ya ce babban burinsa a rayuwa shi ne ‘ya’yan Musulmi kullum su kasance masu tsoron, yana mai karawa da cewa burinsa kullum shi ne "Allah ya shirya mana ‘ya’yanmu."