Man City za ta fadada Etihad da zai ci 'yan kallo sama da 60,000

Etihad

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Manchester City na shirin fadada filin wasanta na Etihad, wanda zai ke daukar 'yan kallo sama da 60,000 nan gaba.

Kungiyar wadda ke nazarin yadda za a gudanar da aikin na hangen fadada wajen zaman 'yan kallo daga Arewacin filin na Etihad.

A shekarar 2015 kungiyar ta fadada filin da ya koma daukar 'yan kallo 53,000.

Kungiyar ta ce fatan da take yi shi ne ta bunkasa filin don zama na daya a fannin wasanni a duniya da samar da aiki ga wadanda suke zaune a yankin.

An gayyaci magoya bayan kungiyar, domin su bayar da ra'ayinsu kan wannan tsarin da za a zauna da su a farkon 2023.

Haka kuma kungiyar ta ce za ta samar da damar makin da za a anfana a ranakun wasannin da wadanda ma ba ranar wasannin ake ba.

Tun cikin watan Agusta City ta tabbatar cewar tana tattaunawa da mahukunta, don kara wajen zaman 'yan kallo daga Arewacin filin wasa na Etihad.

Filin wasa na Etihad shi ne na biyar a yawan cin kwallo a manyan filayen da ake buga Premier League.