Barca na zawarcin Alvarez, Bayern Munich na son Onana

.

Asalin hoton, MANCHESTER CITY

An wallafa

Chelsea ta nemi dan wasan Newcastle Alexander Isak amma kungiyar ta gwammace ta sayar da Callum Wilson, yayin da Bayern Munich ke shirin daukar Onana na E

Chelsea ta nemi dan wasan Newcastle Alexander Isak amma sai ta biya sama da fam miliyan 115 domin sayen dan wasan na Sweden mai shekaru 24. (Mail)

Newcastle ba ta son ganin Isak ya tafi, kuma ta gwammace ta sayar da Callum Wilson, yayin da kungiyoyi daga Ingila, da Jamus da Saudiyya ke sha'awar dan wasan na Ingila mai shekaru 33. (Teamtalk)

Barcelona na zawarcin dan wasan gaban Manchester City dan kasar Argentina Julian Alvarez, mai shekara 24. (Sports Spanish)

Asusun Zuba Jarin jama'a na Saudiyya da ya mallaki kungiyoyi hudu na babbar gasar kasar, ya nemi dan wasan Arsenal dan Ghana Thomas Partey, mai shekaru 31. (Cought Offside)

Atalanta ta kai tayin fan miliyan 10 kan dan wasan Everton Ben Godfrey, yayin da wata kungiya da ba a bayyana sunanta ba ta mika tayin fan miliyan 15 kan dan wasan bayan dan Ingila mai shekara 26. (Athletic)

Everton na dab da daukar dan wasan Najeriya Wilfried Ndidi mai shekaru 27 a kyauta idan kwantiraginsa da Leicester ya kare a mako mai zuwa. (Football Insider)

Dan wasan gaban Newcastle Yankuba Minteh ya ki amincewa da komawa Lyon duk da cewa kulob din na Faransa ya amince da daukar dan wasan na Gambia mai shekaru 19 a kan kudi fan miliyan 40. (Sun)

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Brighton na son dauko dan wasan Inter Miami dan kasar Paraguay, mai shekara 21, Diego Gomez. (Talksport)

Crystal Palace na kokarin daukar dan wasan Sunderland dan kasar Ingila, mai shekara 18, Jobe Bellingham. (Fabrizio Romano)

Ipswich na tattaunawa da Hull kan cinikin dan wasan baya na Ingila Jacob Greaves mai shekaru 23. (Athletic)

Bayern Munich na shirin dauko dan wasan Everton Amadou Onana, mai shekara 22, dan kasar Belgium, bayan bata musu ran da aka yi a a kokarinsu na sayen dan wasan Portugal Joao Palhinha, mai shekara 28, daga Fulham. (Liverpool Echo)

Manchester United na zawarcin golan Bayern Munich dan kasar Jamus Maria Luisa Grohs, mai shekara 23, a matsayin wanda zai maye gurbin Mary Earps na Ingila, wnada ke shirin komawa Paris St-Germain. (Florian Plettenberg)

Kungiyar Al-Hilal ta kasar Saudiyya tana duba yiwuwar daukar wani matashin dan wasan gaban Manchester United Alejandro Garnacho, mai shekara 19, wanda a halin yanzu yana Copa America da Argentina. (Express)

Arsenal na shirin rasa dan wasan Stuttgart Serhou Guirassy, ​​dan kasar Guinea mai shekara 28 wnada ke son komawa Borussia Dortmund. (Metro)