Abin da masana suka ce kan batun 'babu farar-hular da ke da ƴancin dukan ɗan sanda ko da ya ci zarafinsa'

Asalin hoton, Getty Images
Daga Ibrahim Isah, BBC Hausa
Masana shari’a a Najeriya sun fara tofa albarkacin bakinsu a kan wani furuci da kakakin rundunar ƴan sandan kasar ya yi cewa babu farar-hular da ke da ƴancin ɗaga hannu ya doki ɗan sanda da sunan rama cin zarafin da wani ɗan sanda ya yi masa.
Kakakin ƴan sandan ya ce idan har hakan ta faru, sai dai wanda ɗan sandan ya ci zarafi ya kai ƙara kotu domin a bi masa kadin hakkinsa.
Sai dai masana sun bayyana cewa wajibi ne a martaba kayan sarki, amma ɗan ƙasa yana iya kare kansa idan aka wuce ƙima wajen cin zarafinsa.
Kakakin rundunar ƴan sandan Najeriya Olumuyiwa Adejobi ya mayar da martani ne a shafinsa na Twitter dangane da wani bidiyo da aka yi ta yaɗawa a shafukan sada zumunta na zamani, inda aka nuna wani na lakaɗa wa wani ɗan sanda duka, har ta kai ga jan sa a ƙasa.
Kakakin ya ce ɗan ƙasa ba shi da hurumi ko ƴancin cacuma ko dukan ɗan sanda ko da kuwa marin sa ɗan sandan ya yi.
Kakakin ya shawarci al’umma da a dinga kai zuciya nesa a guji ramawa - mafi a’ala ma, gara ɗan ƙasa ya kai ƙara ko kukansa ga hukumar ƴan sandan domin a bi masa hakkinsa.
Wannan furuci na kakakin ya janyo ce-ce-ku-ce a kan dacewar ramawar ko rashin ta, inda wasu ke ganin cewa bai kamata a rama ba, wasu kuma na cewa kowa ya yi maka kan kara ka yi masa na itace.
BBC ta tuntuɓi Barista Mainasara Kogo Umar wani Lauya a Abuja don jin ko ɗan ƙasa na da ƴancin taɓa masu sanye da kayan sarki?
Sai ya ce: “Wajibi ne girmama duk wasu alamu na ƙasa, misali tambarin ƙasa da ke kan hular ƴan sanda da kayan sarki, wanda alama ce ta dogarawan ƙasa da tutar da Najeriya da duk wasu abubuwa na hukumar ƙasar.
“Akwai wajibci a ƙarƙashin sashe na 23 da sashe na 24 na ƴan ƙasa su girmama su.
“Da wannan ne suke amfani da damar da suke da ita suke yin abubuwan da suke yi saboda akwai wajibci ga ƴan ƙasa su yi biyayya a kan wannan.
End of Wasu labaran da za ku so ku karanta
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Lauyan ya ce doka ta bai wa ɗan sanda damar amfani da ƙarfi daidai wa daida wajen kama wanda ake zargi.
“Idan ka nemi ka gudu yana da damar da zai iya sa ƙarfi daidai gwarwagwado domin ya kama ka, amma ba a ce ƙrfi na ya hukunta ka ba.
“Kuma yana da damar jama’a su taimaka masa a kama ka. Ko ɗan ƙasa ma wanda ba ɗan sanda ba yana da dama a doka idan ya ga wani ya yi laifi ya kama shi ya miƙa wa ƴan sanda.
“Amma ba a ce a yi wa mutum duka kamar na yanke hukunci ba – a’a domin duk irin laifin da mutum ya yi ana kan matakin ana zargi ne,” in ji masanin.
Sai dai Barista Mainasara Kogo ya ce idan ɗan ƙasa ya fahinci jami’in tsaro na neman wuce iyakokinsa ko naƙasa shi ba gaira ba dalili, to yana iya kare kansa.
Ya ce “Idan ka ga yana neman ya ci maka mutunci ko ya wuce gona da iri to kana iya kare kanka.
“Abu na farko da za ka tambaye shi shi ne ya ba ka takardar sammaci wato warrant.
“Idan ba shi da wannan iznin to ka gaya masa a matsayin girmama wannan kayan sarki da yake sanye da su, to ka wuce in bi ka mu tafi tare ba dole sai na shiga motarka ba, shi ma ba dole ya shiga taka ba.”
Mainasara Kogo ya ci gaba da cewa “Ka tambaye shi ma shin ina shaidar cewa shi ɗan sanda ne kamar katin shaida ko lambarsa ta ɗan sanda, wanda daga nan kana iya amfani da lambarsa ta ɗan sanda ka kai shi ƙara a hukuma ta gaba da shi.
“Idan ya ƙi to kana da ƴancin da kai ma za ka ja kulki ka buge shi, ka da kuma bugun da za ka masa ya wuce wanda shi ya yi maka. A nan kuma ka ɓallo wani laifin ne,” ya ƙara da cewa.
Duk da cewa rundunar ƴan sandan na kwaɗaita wa mutanen da ke zargin jami’anta sun ci zarafin su da su kai mata ƙara, wasu na ganin cewa da wuya irin wannan tayin ya samu karɓuwa - sai hukumomin ƴan sandan sun gamsar da al’umma cewa za bi kadun nasu a zahiri.
Saboda wasu da dama na kukan cewa ko sun kai kuka ba abin da ke biyo baya face jan-kafa da nuƙu-nuƙu - wani lokaci ma sai reshe ya juya da mujiya.










