Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Forest ta karshen teburin Premier ta ci Liverpool
Nottingham Forest ta yi nasara a kan Liverpool da ci 1-0 a wasan mako na 13 a gasar Premier League da suka kara a City ground ranar Asabar.
Taiwo Awoniyi, tsohon dan wasan Liverpool, wanda ya bar kungiyar a 2021 ba tare da buga mata wasa ba, shi ne ya ci kwallon a minti na 55.
Awoniyi ya zama dan wasan Nottingham Forest na farko da ya ci kwallo a wasa uku da ya yi a gida wato a City ground.
Shi ne ya fara ci wa kungiyar kwallo a wasan da ta ci West Ham da fara kakar bana, na farko a City Ground tun bayan shekara 23 rabon da ta buga Premier League.
Dan wasan ya ci kwallo a karawar da Fulham ta ci Forest 3-2, sannan wannan dayan da ya zura a ragar Liverpool.
Liverpool ta yi rashin nasara uku a wasa 11 da ta buga a Premier League ta bana, wadda wasa biyu kacal ta yi rashin nasara a karawa 38 a bara.
Bayan tashi daga wasan an yi murna a filin City ground, sakamakon nasarar da ta yi, kuma hakan ya sa ta bar matakin karshe a teburin Premier.