Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Klopp ya musanta batun baya iya haura shekara takwas a kungiya
Jurgen Klopp ya yi watsi da batun cewar rashin kokarin da yake a bana a Liverpool ya samo asali kan sallon koci da yake yi a kaka bakwai.
Ranar Asabar dan kasar Jamus ya cika shekara bakwai da aka nada shi jan ragamar kungiyar Anfield, wanda ya maye gurbin Brendan Rodgers.
Kungiyoyi biyu da Klopp ya ja ragama a baya wato Mainz da Borussia Dortmung ya kasa jan ragamarsu zuwa kaka ta takwas kowacce.
''Yana yin ya banbanta. Shekara bakwai ba wai ban yi shiri bane, ko kuma na gaza.''in ji Klopp.
''Na horar da Mainz, kuma bayan shekara uku, sai muka samu shiga Bundesliga, amma shekara uku a gasar sai muka fadi.
''Mun kara daukar sabon salo a kaka daya, amma kungiyar sai ta bukaci sauyi inda 'yan wasa da yawa suka barmu, domin suna son buga Bundesliga.''
Yadda ya yi aiki da Dortmund, ya kara da cewar ''Nan take na koma Dortmund kuma abubuwan sun tafi yadda ya kamata. A shekara bakwai mun shiga yanayin da kungiyoyi ke ta sayen 'yan wasanmu.
''Aiki ne mai dan karen wahala, wanda kana gini ana mayar da hannun agogo baya.''
A kakar farko da Klopp ya karbi aikin horar da Dortmund, kungiyar tana daf da faduwa daga Bundesliga a lokacin Kirsimeti, sai dai ta kammala a mataki na bakwai a teburi a kakar.
Klopp ya ce ''Na kwan da sanin na bar aiki karo biyu a baya kowanne bayan kaka bakwai, amma wannan karon yanayin da ban yake da na baya.
Idan har za a tsaya a yi duba na tsanati da akwai banbancin aikin da na yi a kungiyoyin Jamus da wanda yanzu nake gudanarwa a Liverpool''.
Liverpool tana ta 10 a teburin Premier League da maki 10, bayan buga wasa bakwai - za ta kara da Arsenal ranar Asabar a Emirates.
Lahadi mai masa takwas tana mataki na biyu a teburin babbar gasar tamaula ta Ingila, mai maki 21 da zarar maki biyu tsakaninta da Manchester City ta daya.
Ranar Asabar Manchester City ta ci Southampton 4-0, dalilin da ya sa ta koma ta daya a kan teburin Premier League kenan.