Me ya sa aka dage wasan Arsenal da Man City a Premier League?

An wallafa

An dage wasan da ya kamata Arsenal ta karbi bakuncin Manchester City a karawar mako na 12 a gasar Premier League ranar Laraba.

Arsenal wadda ta ci Leeds United 1-0 a makon jiya tana ta daya a kan teburin babbar gasar tamaula ta Ingila mai maki 27.

City mai rike da kofin bara kuwa wadda ta yi rashin nasara da ci 1-0 a hannun Liverpool a Anfield ranar Lahadi tana ta biyu da tazarar maki hudu tsakaninta da Gunners.

Ranar Alhamis Gunners za ta karbi bakuncin PSV Eindhoven a wasa na biyu a cikin rukuni da ya kamata su buga tun ranar 15 ga watan Satumbar 2022.

Hakan ya biyo bayan zaman makokin rasuwar Sarauniya Elizabeth II.

Arsenal da PSV Eindhoven sun kara sau shida a tsakaninsu a gasar zakarun Turai, inda Gunners ta yi nasara a biyu da canjaras uku, PSV Eindhoven ta ci daya.

Wasannin da suka buga a gasar zakarun Turai a tsakaninsu:

2006/2007

Champions League Laraba 7 ga watan Maris 2007               

  • Arsenal 1 - 1       PSV Eindhoven 

Champions League Talata 20 ga watan Fabrairun 2007 

  • PSV Eindhoven  1 - 0       Arsenal

2004/2005

Champions League Laraba 24 ga watan Nuwambar 2004    

  • PSV Eindhoven  1 - 1       Arsenal

Champions League Talata 14 ga watan Satumbar 2004 

  • Arsenal 1 - 0       PSV Eindhoven 

2002/2003

Champions League Talata 12 ga watan Nuwambar 2002    

  • Arsenal 0 - 0       PSV Eindhoven 

Champions League Laraba 25 ga watan Satumbar 2002    

  • PSV Eindhoven  0 - 4       Arsenal

Teburin rukunin farko a Europa League:

  • Arsenal          3            3            0            0            3            6            1            5              9
  • Eindhoven    3            2            1            0            3            11          2              9            7
  • Bodo/Glimt  4            1            1            2            2            3            6              -3           4
  • FC Zurich      4            0            0            4            2            3            14           -11         0