An dakatar da Ronaldo na wasa ɗaya

Ronaldo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ronaldo ya zura kwallo 42 cikin wasa 48 tun lokacin da ya koma Al-Nassr
An wallafa

An dakatar da ɗan ƙwallon Al-Nassr Cristiano Ronaldo daga buga wasa ɗaya saboda tanka wa ƴan kallo a wasan da suka doke Al-Shabab a gasar ƙwallon Saudiyya.

Magoya bayan Al-Shabab sun yi ta ihun sunan 'Messi' - mutumin da ake kallo babban abokin hamayyar Ronaldo.

Al-Nassr ta samu nasara a wasan da ci uku da biyu a birnin Riyadh.

Kyaftin ɗin Portugal mai shekaru 39, ya rufe kunnensa sannan ya yi wata alama da hannu.

Hukumar ƙwallon Saudiyya - SAFF ta kuma ci tarar Ronaldo ɗin Riyal dubu 30.

Kwamitin ɗa'a na ƙwallon Saudiyyar ya ce Ronaldo ba zai iya ɗaukaka ƙara ba.

Ronaldo ya koma Al-Nassr ne daga Manchester United a watan Disamban 2022 kuma bayanai sun ce ya fi kowanne ɗan kwallo karɓar albashi.

Ya zura ƙwallo 20 a cikin wasa 22 a kakar bana kuma Al-Nassr ce ta biyu a kan teburin gasar inda Al-Hilal ke kan gaba.