Man United na shirin korar Ronaldo daga ƙungiyar

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United na duba hanyoyin da za ta bi da zimmar soke kwantaragin Cristiano Ronaldo a kulob ɗin ko kuma ɗaukar matakin shari'a a kansa.
Wasu mahukunta a United sun amince cewa bai kamata Ronaldo ya sake buga wa ƙungiyar wasa ba a ƙarƙashin mai horarwa Erik ten Hag bayan kakkausar sukar da da ya yi wa kocin a hirarsa da Talk TV.
Wata bakwai ne ya rage kafin yarjejeniyarsa ta zo ƙarshe a United, wadda ke ba shi albashin fan 500,000 duk mako.
A ranar Juma'a United ta fitar da sanarwar cewa sun fara "shirin da ya dace" na mayar da martani kan soke-soken da Ronaldo ya yi musu.
Ƙungiyar ka iya katse kwantaragin nasa, abin da zai sa ya koma wata ƙungiyar a kyauta idan aka buɗe kasuwar saye da musayar 'yan wasa a watan Janairu mai zuwa.
An fahimci cewa ba sa son su biya ɗan wasan mai shekara 37 maƙudan kuɗaɗe saboda karya yarjejeniyar ganin yadda suka ji da zargen-zargen da ya yi kan masu kulob ɗin.
Ƙungiyar na son ta gama da matsalar cikin sauri don kar lamarin ya kai har zuwa watan Janairu.
A hirar da ya yi, Ronaldo ya ce ƙungiyar ta "yaudare shi" kuma ya ce ba ya "mutunta" mai horarwa Erik ten Hag saboda shi ma "ba ya girmama shi". Ya ƙara da cewa wasu na son su tilasta masa ficewa daga kulob ɗin.
Ronaldo zai jagoranci tawagar ƙasarsa Portugal a wasannin Kofin Duniya bayan sun isa Qatar ranar Juma'a.
Za su buɗe wasa tare da Ghana a Rukunin H ranar Alhamis.











