'Yadda Najeriya ta ƙi miƙa Tchiroma Bakary ga hukumomin Kamaru'

Asalin hoton, Getty Images
Rahotanni na tabbatar da cewar jagoran adawa na Kamaru Issa Tchiroma Bakary na ƙarƙashin kulawar jami'an tsaron Najeriya a garin Yola na jihar Adamawa, bayan da hukumomin ƙasar suka ƙi amincewa da buƙatar takwarorinsu a Kamaru na miƙa shi.
Rahotannin sun tabbatar da cewa wasu jami'an tsaron Kamaru na musamman ne suka yi yunƙuri "sace" tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar a ranar 2 ga watan Nuwamba, tare da taimakon jami'an tsaron Najeriya.
Jami'an tsaron Kamaru sun bayyana wa na Najeriya cewa Tchiroma "mai laifi ne mai hatsari".
"Amma a lokacin da jami'an tsaron Najeriya suka gano ko wane ne, sai suka ƙi amincewa da shirin miƙa shi. A yanzu yana ƙarkashin kulawar jami'an tsaron Najeriya, abin da ya hana duk wani yunƙuri na sake kama shi, kamar yadda bayanai suka nuna.
Tchiroma, wanda ya yi takarar a zaben shugaban ƙasar na ranar 12 ga watan Oktoba, ya kasance ƙarƙashin ɗaurin talala a gidansa da ke birnin Garoua, a arewa maso nisa ta Kamaru, tun daga ranar da aka gudanar da zaɓen.
Yunƙurin mayar da shi Kamaru ya zo ne kwana daya bayan ministan harkokin cikin gida na Kamaru Paul Atanga Nji ya yi gargadin cewa za a gurfanar da Tchiroma Bakary a kotu kan zargin "tunzurarwa domin tayar da hankali", a lokacin wani taron manema labarai da ya kira a birnin Yaounde.
Atanga Nji ya nanata sau da dama a lokacin taron cewa Tchiroma ya karya doka bayan ya bayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa kwana ɗaya bayan kammala zaɓe, wani abu da ministan ya bayyana a matsayin abu ne da ya keɓanta kacokan ga Majalisar Kundin Tsarin Mulki ta ƙasar.
Jaridar Cameroun Actuel ta ruwaito cewa an ga wasu sojoji guda huɗu zuwa shida cikin kaya na shirin ko-ta-kwana, ɗauke da bindigogi, suna sauka a sassa daban-daban na unguwar Marouare, inda Tchiroma ke zama. Sai dai ba a san manufarsu ba.
Jami'an tsaron sun kafa cibiyoyin bincike, kimanin mita 50 daga gidan Tchiroma, wani mataki da ake kallon yunƙuri ne na hana shi fita.
Jaridar ta bayyana cewa wannan ba shi ne karon farko da ake ceto Tchiroma daga wani abu da ake wa kallon hatsari ba. A ranar da aka gudanar da zaɓe, jami'an tsaro sun tare motar da ke ɗauke da Tchiroma.
Sai dai magoya bayansa sun ƙwace shi, bayan da suka yi zaton cewa za a iya cutar da shi.
Me ya biyo baya?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Tuni dai Paul Biya ya yi gargaɗi game da mummunan matakin da za a ɗauka kan waɗanda suka tayar da hargitsi bayan zaɓen shugaban ƙasar.
Biya, wanda ya lashe kashi 53.66% na ƙuri'un da aka kaɗa, kamar yadda hukumomi suka bayyana, ya ce Kamaru ba za ta ci ribar komai ba idan ta faɗa cikin tashin hankali.
"Kamaru ba ta buƙatar faɗawa cikin rikicin bayan zaɓe wanda zai iya yi mata illa, kamar yadda aka yi a wasu aurare," in ji Paul Biya, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X a ranar 13 ga watan Nuwamba.
Ana kallon bayanin nasa a matsayin martani ga ikirarin da Tchiroma ke yi yin nasara a zaɓen.
A daidai ;lokacin ne kuma Babban hafsan sojin ƙasar, Laftanar Janar Rene Claude Meka ya tsawaita sintirin tabbatar da tsaro na bayan zaɓe a akasar zuwa ranar 10 ga watan Disamba, bayan bayyana cewa akwai barazanar tashin-tashina.
Tuni dai aka rantsar da shugaba Paul Biya - wanda ya fi kowane shugaban ƙasa tsufa a duniya - a wa'adin mulki karo na takwas.










