Ronaldo ba zai buga wasa da Najeriya ba

Asalin hoton, Getty Images
Tauraron ɗan wasan ƙwallon ƙafa na tawagar Portugal Cristiano Ronaldo ba zai buga wasan da ƙasarsa za ta fafata da Najeriya ba a yammacin Alhamis sakamakon ciwon ciki da yake fama da shi.
Kocin tawagar Portugal, Fernando Santos, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labaraia da aka yi ranar Laraba gabanin wasan na sada zumunta.
"Ba zai buga wasan [Najeriya] ba gobe [Alhamis]. Ya rasa ruwan jiki sosai saboda ciwon ciki da yake fama da shi kuma ba ya atasaye," in ji shi.
Ya ƙara da cewa "yana ɗakinsa yana hutawa da kuma samun sauƙi".
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Tawagar Super Eagles ta Najeriya za ta fafata da Portugal a wasan share fagen gasar Kofin Duniya ta 2022 da za a fara a Qatar.
Za a buga wasan a Filin Wasa na José Alvalade da ke birnin Lisbon na Portugal ranar Alhamis da ƙarfe 7:45 agogon Najeriya da Nijar.
Najeriya ba ta samu gurbin shiga Kofin Duniya ba sakamakon rashin nasarar da ta yi a hannun babbar abokiyar hamayyarta Ghana.
Cristiano Ronaldo na ci gaba da yamutsa hazo a duniyar ƙwallon ƙafa a makon nan sakamkon hirar da ya yi da Talk TV, inda ya zargi ƙungiyarsa ta Manchester United da "yaudarar sa".
Kazalika, ya ce "ba na girmama koci Eric ten Hag saboda shi ma ba ya mutunta ni".











