Renard ya maye gurbin Mancini a matsayin sabon kocin Saudiyya

Herve Renard

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

An sake naɗa Herve Renard a matsayin kocin tawagar ƙwallon ƙafan Saudiyya bayan tafiyar Roberto Mancini.

Renard ɗan ƙasar Faransa ya karɓi ragamar horar da ƴan wasan ƙasar Saudiyya daga watan Yulin 2019 zuwa watan Maris na 2023 kuma ya jagoranci tawagar zuwa ga nasara mai ban mamaki a kan Argentina a matakin rukuni na gasar cin kofin duniya ta Qatar 2022.

Kocin mai shekaru 56 ya ajiye aiki, inda ya jagoranci tawagar matan Faransa a gasar cin kofin duniya ta 2023 da kuma gasar Olympics ta bana.

Mancini ne ya maye gurbinsa a Saudiyya, amma yanzu ya sake dawowa bayan ɗan Italiyan ya soke kwantiraginsa da hukumar ƙwallon ƙafar Saudiyya.

Mancini, mai shekaru 59, ya bar aikinsa na kocin Italiya kuma ya zama kocin Saudiyya a watan Agustan 2023.

"Na dawo," in ji Renard a wani bidiyo, wanda aka wallafa shafin X na hukumar ƙwallon ƙafa ta Saudiyya.

“Ban yi niyyar ficewa ba, amma idan ƙasarka ta ƙwanƙwasa ma ka ƙofa, dole ne ka amsa.

"Ban kammala aikin da da na fara a Saudiyya ba tukuna."

Renard zai fara aiki a karo na biyu ne da wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya inda tawagarsa za ta fafata Australia da kuma Indonesia a watan Nuwamba.