Falasɗinawan da sojojin Isra'ila suka daka wa ɗan karen duka

- Marubuci, Adnan El-Bursh
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Arabic
- Aiko rahoto daga, Rafah, Gaza
- An wallafa
Falasdinawa shidan mazauna Gaza sun ce, sojojin Isra'ila sun yi musu dukan kawo wuka, a tsawon kusan wata guda da suka shafe a tsare a hannunsu.
Daya daga cikinsu ya ce sojojin sun harbe shi a kafar hagu, kuma aka yanke masa kafar da kafafuwan wasu mutanen da ake tsare da su.
A karkashin dokar yaki, duk wanda aka kama ya kamata a tafiyar da al'amuransu cikin mutunci.
Sai dai kakakin rundunar ma'aikarar tsaron Isra'ila (IDF) ya shaida wa BBC cewa, basu da isassun bayanan da zasu aiwatar da bincike a kan zargin da mutumin ya yi na cewa an yanke masa kafa.
Mai magana da yawun rundunar ta Isra'ila ya kuma ce, kasar na mutunta dokokin kasa da kasa.

A ranar Alhamis 14 ga watan Disamba ne Isra'ila ta saki mutanen, a bakin iyakar Kerem Shalom da ya hada kasar ta Isra'ila da kuma Gaza.
Daga nan ne suka samu kulawa a asibitin Shahidi Mohammed Yusuf al-Najjar, da ke Rafah a kudancin Gaza.
Wasu gwamman wadanda Isra'ilar ta sako suna wannan asibitin, amma mutane bakwai ne kawai suka yarda suka yi magana da BBC.
Hudu daga cikinsu na zaune a kan wani gadon asibiti, yayin da na biyar dinsu ke tsaye a gefensu.
Dukkaninsu na sanye da riga da wando ruwan toka, kuma sun nuna wuyan hannayensu masu alamun jin ciwo, wasu kuma sun kumbura ga kuma raunuka a jikinsu.
Wasu kuma har zuwa wannan lokacin, akwai igiyar robar ankwa da Isra'ila ta yi amfani da shi wajen daure su a lokacin da ta tsare da su.

Mohammed Dawood ya ce an kama shi ne a lokacin da yake kaura zuwa kudancin Gaza, kamar yadda Isra'ila ta umarce su da yi.
"Mun fito daga Beit Lahiane da ke arewa, muna tafiya zuwa kudanci ta hanyar da aka amince da ita" In ji Mohammed
"Sai sojin Isra'ila suka kama mu. Suka yi mana tambayoyi. Suka ce ku 'yan Hamas ne? Ku mayakan jihadi ne?"
Ya ce an tsare shi na tsawon kwanaki 26, amma daga bisani aka sake shi domin ba a samu komai a tare da su ba."

A ranar 14 ga watan Nuwamba ne rundunar tsaron Isra'ila ta sanar da cewa ta bude wasu hanyoyi na wucin-gadi da tace ta yarda Falasdinawa bi, domin yin kaura daga arewaci zuwa kudancin Gaza.
Isra'ila ta bayyana hanyoyin da cewa "hanyoyi ne masu aminci" domin samar da kayan agaji ta babban titin Salah al-Din.
Sai dai an samu rahotannin dake cewa sojojin sun dinga tantance mutane, suna tsare wasu.
"An daure ni kuma aka rufe mini idanu da wani kyalle, kamar yadda aka yiwa sauran maza" A cewar Mohammed Dawood.
"Sun ci zarafinmu, sun tofa mana yawu kuma sun ci mutuncinmu.
Sannan sun yi wa dukkaninmu duka.
"Idan wani ya ce bashi da lafiya ko kuma an yanke masa kafa, sai sojin su ce masa 'ka ma mutu a nan.'
"Sai su rataye mutum da ankwar da suka sa masa. "

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Mai magana da yawun rundunar sojin Isra'ila ta IDF ya musanta zarge-zargen.
"Game da alamun raunin da mutanen da muka tsare suka samu sakamakon sa musu ankwa mun bayyana cewa, muna sa musu ankwa ne saboda irin hatsarin da suke da shi da kuma lafiyarsu." A cewar wata sanarwa daga rundunar.
"Ba a taba rataye kowa ta wuyan hannusa ba kwata-kwata, a wurin da aka ajiye su."
Mohammed ya ce sun yi amfani da bargo daya dukansu, kuma ana barinsu a waje suna shan ruwan sama.
Yayin da ake basu abinci da ruwan sha kadan.
Sai dai rundunar sojin ta Isra'ila ta sake watsi da wannan zargi, tana mai cewa ana bayar da abinci sau uku a rana da ruwa da kuma kula da lafiyar wadanda ta ke tsare da su.
Babu wanda ya san adadin mutanen da sojojin Isra'ila suka tsare a Gaza da ma wasu wuraren da suke rike da mutane.
Wannan batu yana jan hankali sosai tun bayan fitan wani bidiyo daga Beit Lahia, a farkon wannan watan.
Bidiyon ya nuna gwamman Falasdinawa maza a tube, an barsu daga su sai dan kamfai, suna zaune cikin sahu, yayin da sojojin Isra'ila ke gadinsu.

Mutum na shida, Mahmoud Abu Husein, na zaune a wata kujera a wata hanyar da ake wucewa a cikin asibitin.
Yana da furfura kuma bashi da kafar dama, duk ga jini ya bata wandonsa daidai inda aka nade dungun.
"Ina cikin gidana, na gaya musu cewa bani da lafiya, ni dattijo ne mai shekaru 62 a duniya," Ya shaida wa BBC, inda ya kara da cewa daga sansanin al-Shati yake dake arewacin Gaza.
"Sai suka ce mini a'a sai ka gano mana inda Hamas take da inda take tsare da wadanda take garkuwa da su.
"Da na ce musu ban sani ba, sai suka harbi kafata, sannan daga bisani suka yanke ta.
"Sai suka sa na sanya hannu a wata takardar da ke cewa, bana iya komai da kafar."
Rundunar sojin Isra'ila ta ce bata da isassun bayanan da za ta iya bincike a kan wannan al'amari.

Wasu likitoci da suka nemi a boye sunayensu a asibitin sun ce, mutane sun iso asibitin a cikin wani mummunan hali.
Sun ce biyu daga cikinsu na ci gaba da samun kulawa, ciki har da Mahmoud .
Wani dattijo, Mohammed Yusuf Ali Abu Shamla, wanda shi ma yake jira a daya daga cikin hanyoyin dake cikin asibitin, ya fito ne daga unguwar Zeitoun da ke gabashin birnin Gaza.
Mista Shamla, shi ne mutum na bakwai da BBC ta yi magana da shi, kuma kamar sauran yana sanye ne da riga da wando ruwan toka.
Sai dai da alamu shi sojin Isra'ilan sun tsare shi ne, bayan kama wadancan mutanen.

"Motar rusau ta fara rusa gidana, ni da wasu mutane 40 na ciki," Ya bayyana wa BBC. "Mata na ta ihu. Muka fice hannayenmu a sama."
Ya ce an kama shi da wasu su shida: 'ya'yansa maza uku da 'ya'yan 'yan uwansa biyu da kuma dan uwansa.
"Sai suka ce mu cire kayanmu. Me kuke nufi da cewa mu cire kayanmu? Mun ji kunya amma dole muka cire rigunanmu. In ji shi.
"Suka ci gaba da sanya mu cire komai dake jikinmu, har sai da ya rage mana dan kamfai."
Rundunar Sojin Isra'ilan ta ce ta bukaci su cire kayansu ne don tabbatar da cewa basa dauke da jigidar abubuwa masu fashewa ko kuma wani makami.

Mista Shamla ya ce an tsare su tsawon kwanki uku a Gaza, kafin aka kai su Isra'ila.
Ya ce yana kokarin gano inda iyalansa suke saboda shi kadai aka sako.
"Ban san ida sauran suke ba, kaina kawai na sani."






