Fifa za ta hukunta Uruguay da 'yan wasanta hudu

Uruguay

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Fifa za ta hukunta hukumar kwallon kafar Uruguay da 'yan wasanta hudu kan halin rashin da'a a karawa da Ghana a Gasar Cin Kofin Duniya.

Uruguay ce ta doke Ghana 2-0 a wasan karshe a rukuni na takwas a Gasar Cin Kofin Duniya ranar 2 ga watan Disambar 2022.

Uruguay ta karkare a mataki na uku a rukuni na takwas duk da cin Ghana da ta yi, inda Portugal da Koriya ta Kudu suka kai zagayen gaba.

'Yan wasan Uruguay sun harzuka bayan tashi daga wasan, inda suka kalubalanci alkalin wasa da mataimakinsa kan zargi hana su bugun fenariti, bayan karo da aka yi tsakanin Alidu Seidu da Darwin Nunez.

Wadanda Fifa za ta hukunta daga Uruguay sun hada da Jose Maria Gimenez da Edinson Cavani da Fernando Muslera da kuma Diego Godin.

Haka kuma hukumar kwallon kafar Uruguay na fuskantar hukuncin rashin da'a da nuna banbanci.

Haka kuma Fifa na bincikar hukumar kwallon kafar Serbia a wasan da tawagarta ta buga da Switzerland a karawar karshe a rukuni na bakwai da suka tashi 3-2.

Fifa ba ta fayyace laifin da Serbia ta aikata ba, amma an umuarci magoya bayan tawagar da su daina rera wakar banbanci a lokacin wasan.