Ana tunanin sayar da Manchester United

Asalin hoton, Getty Images
Iyalin Glazer da suka mallaki kungiyar kwallon kafa ta Manchester United sun ce suna tunanin sayar da kulob din yayin da da suke “ neman wasu hanyoyi masu muhimanci.”
Amurkawan sun sayi kungiyar a kan fam miliyan 790 a shekarar 2005.
Wannan na zuwa ne bayan tsawon shekarun da magoya bayan kungiyar suka rika nuna rashin amincewa da mallakarsu.
Sanarwar da aka fitar ta ce kwamitin gudanawar kungiyar, “ zai yi nazari a kan wasu hanyoyi, ciki har da sabbin masu zuba jari a cikin kungiyar, ko wasu hada -hadar da suka shafi kamfanin”
A 2012 iyalin Glazers sun sayar da kashi 10 cikin 100 na hannun jarinsu a kasuwar hada hadar hannayen jari kuma sun kara sayar da hannun jari a wasu shekarun bayan nan.
"Yayin da muke neman ci gaba da gina tarihin nasarar kungiyar Manchester United, kwamitin gudanarwa ya bayar da izinin yin cikakken nazari kan wasu hanyoyin masu muhimanci da za a iya amfani da su.” In ji shugabannin kamfanin watay Avram Glazer da Joel Glazer.
“ Za mu yi nazari kan zabin da ke akwai don tabbatar da cewa mun yi abin da ya fi dacewa domin amfanin magoya bayanmu tare kuma da ganin cewa kungiyar ta samu damarmakin habaka a yau da kuma nan gaba.”
" A karkashin wannan tsarin za mu mayar da hankali wajen ganin mun kare muradun magoya bayanmu, masu zuba jari da sauran masu ruwa da tsaki."

Asalin hoton, BBC Sport
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Rabon Manchester United, wadda ita ce ta biyar a gasar Firimiya da daukar kofiin gasar tun bayan 2013 kuma ba ta sake daukar kofin Europa da EFL ba tun bayan 2017.
An yi ta zanga-zangar nuna rashin amincewa da yadda iyalin Glazer suka mallaki kungiyar a shekarun baya-bayan nan, ciki har da wadda aka yi a watan Mayun 2021 wadda ta sa aka dakatar da wasan da kungiyar za ta yi da LiverPool.
Dubban magoya bayan kungiyar sun yi tattakki zuwa filin wasan Old Trafford domin nuna rashin amincewasu a kakar bana, a watan Augusta.
Manchester United na cikin wani bangare na sabuwar gasar Zakarun Turai ta Super league wadda aka kirkiro da ba ta yi nasara ba , wadda kuma ta ruguje a watan Afrilun 2021.
Mataimakin shugaban kungiyar Joel Glazer daga bisani ya nemi afuwa sakamakon rikicin da ya biyo baya.
Tun bayan wannan lokaci ya rika ganawa da magoya bayan kungiyar a taruka kuma ya yi alkawarin bai wa magoya bayan damar sayen jarin kungiyar.
Kyafin din Portugal Cristiano Ronaldo, wanda ya bar Manchester United da gaggawa a ranar Talata, ya soki masu kungiyar a wata hira mai cike da ce-ce-ku-ce da ya yi a makon da ya gabata yana mai cewa iyalin Glazer,” ba su damu da kulob din ba” a bangaren wasanni.
Yunkurin sayar da Manchester United na zuwa ne bayan da shugaban kungiyar Liverpool Tom Werner ya ce kamfanin wasanni na Fenway Sports Group ya fara duba hanyoyin sayar da kulob din.
Wani rahoto Bloomberg da aka fitar a watan Augustan 2022 ya ce iyalin Glazer a shirye suke su sayar da hannun jarin na wadanda ba su da yawa a kungiyar.
Attajirin nan dan kasar Birtaniya Sir Jim Ratcliffe ya nuna sha'awar sayen kungiyar kafin ya bayyana a watan Oktoba cewa iyalin Glazaer sun fada masa cewa ba za su sayar ba.
A watan Mayu ne wani babban kamfani karkashin jagorancin mai saka hannun jari Ba’amurke Todd Boehly da kuma wani kamfani da ake kira Clearlake Capital suka sayi Chelsea kan fam biliyan 4.25











