Ronaldo zai bar Manchester United ba tare da bata lokaci ba

Asalin hoton, PA Media
Dan wasan gaban Portugal Cristiano Ronaldo zai bar kulob din Manchester United ba tare da wani bata lokaci ba.
Hakan ya biyo bayan wata hira da ya yi wadda ta jawo takaddama, inda dan wasan mai shekara 37 ya soki kungiyar har da cewar baya martaba Erik ten Hag.
United da wakilan Ronaldo duk sun tabbatar da raba gari a tsakaninsu.
A wata sanarwa da Manchester United ta fitar ta ce ''Tana godiya kan rawar da dan wasan ya taka a karo biyu da ya yi a Old Trafford.
Ta kuma yi masa ''Fatan nasara da shi da iyalansa kan abin da zai fuskanta a nan gaba''.
Ta kara da cewar ta mayar da hankali kan yadda za ta marawa Erik ten Hag baya da aiki tare, domin mayar da kungiyar kan ganiyar da take bukata''.
Ronaldo yana tare da tawagar Portugal a Qatar domin buga Gasar Cin Kofin Duniya, wanda zai yi kyaftin a karawa da Ghana ranar Alhamis a rukuni na takwas.
''Bayan da muka tattauna da Manchester United mun cimma yarjejeniyar kowa ya kama gabansa,'' in ji wani bayani daga bangaren Ronaldo.
Ya kara da cewar ''Ina kaunar Manchester United da magoya bayanta, hakan ba zai taba sauya wa ba.
Kuma lokaci ne ya yi da zan fuskanci wani kalubalen a fannin tamaula.
''Ina yi wa kungiyar fatan samun nasara a sauran wasannnin kakar bana da ta nan gaba.''
A wata hira da TalkTV a makon jiya, Ronaldo ya ce ''An yaudare ni a kungiyar'' ya kuma kara da cewar ana ta kokarin sai na bar United ta kowanne hali.
Ya kara da cewar ba wani gagarumin ci gaba a kungiyar tun bayan da Sir Alex ya yi ritaya daga horar da kungiyar a 2013.
Ranar Juma'a United ta fitar da bayanin cewar tana duba hanyar da za ta mayar da martani ga hirar da aka yi da Ronaldo.











