Shugaba Macron na rangadi a Afirka

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya je Gabon a ziyarsa ta Farko da yake kawo wa wata nahiyar Afirka tun bayan kaddamar da sabbin tsare-tsare kan alakar kasarsa da nahiyar.
Shugaba Macron ya je Gabon ne domin halartar taro kan muhalli da aka jima ana shiryawa.
Wannan rangadi na zuwa ne sama da mako guda bayan dakarun Faransa sun kawo karshen aikinsu a Burkina Faso.
Sannan ana cigaba da samun karuwar kin jinin Faransa da kuma karuwar gogayya tsakanin manyan ƙasashen duniya da ke son karfafa alaƙa ko tasiri a nahiyar.
Sai dai rangadin da ya kawo Afirka na zuwa ne adaidai lokacin da ake sake samun sukurkucewar alaƙa tsakanin kasasarsa da kasashen da suka raina.

Asalin hoton, AFP
Sojojin Faransa sun janye daga Burkina Faso da Mali bayan samun rashin jituwa da masu masaukinsu.
Amma a yanzu Mista Macron burinsa shi ne rage ayyukan dakarun sojinsa a Afirka da mayar da hankali wajen gina wata alaƙa ta daban mai karfi.
Kafin ya soma wannan ziyarar shugaban ya ce Faransa a yanzu burinta shi ne mayar da hankali domin karfafa alaƙa da inganta kawance da nahiyar Afirka.
Sabbin tsare-tsarensa kan Afirka za su bada fifiko a fanin sana'o'i da dawo da kadarorin da aka sace da sake zuba hanayen-jari sama da abin da aka san Faransa a nahiyar.
Bayan Gabon ana kuma sa ran ziyartasa zata kai shi kasashen Congo da Angola.









