Ko ɗaure masu liƙin kuɗi a wurin buki zai sanya ƴan Najeriya shiga taitayinsu?

Takaudun kuɗin naira

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Takardun kuɗin naira
    • Marubuci, Mansur Abubakar
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Kano
  • An wallafa

Ɗaya daga cikin ginshiƙan bukukuwa a Najeriya na fuskantar barazana.

Da zaran amarya da ango suka shiga tsakiyar fage suna tattakawa, abokan arziƙi kan miƙe tsaye su matsa kusa suna liƙa musu kuɗi.

Kiɗa na tashi, su ma takardun kuɗi na tashi - ana yi wa amarya da ango ruwan takardun kuɗi.

Kuɗin da ake liƙawa na zuba a ƙasa, inda daga ƙarshe za a kwashe kuɗin a tattara a miƙa wa amarya da ango ko kuma a biya mawaƙa.

"Ta yaya zan je buki ba tare da na liƙa wa amarya da ango kuɗi ba? Zai zama tamkar ba na son su ke nan," kamar yadda wata ta shaida a wa BBC a Kano.

Angon da aka yi bikin nasa, wanda bai yarda a bayyana sunansa ba domin gudun kada a kama shi, ya shaida wa BBC cewa yana kallon hotuna da bidiyon da aka ɗauka na yadda aka riƙa yin liƙi a lokacin bikinsa "saboda abin na burge ni".

Matsalar ita ce a yanzu gwamnati ta fara kamen mutanen da ke liƙa kuɗi a lokacin bukukuwa.

Tuni ma aka kama wasu mashahuran mutane a ƙasar aka aika su gidan gyaran hali.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Duk da cewa liƙin kuɗi lokacin buki abu ne da mutane kan yi - ko dai domin nuna cewa suna da wadata ko kuma domin taimako, amma wannan al'ada abu ne da ya saɓa wa dokokin Najeriya: wato cin zarafin takardar kuɗin Najeriya ta naira.

Dokar Babban bankin Najeriya ta 2007 ta ce: "Ba tare da wata tantama ba, watsawa, rawa a kai ko taka naira ko duk wata takardar da banki ya bayyar - a lokacin bukukuwa ko taruka ko ma nene ne, ya zama cin mutuncin kuɗi".

Hukuncin hakan ba zai gaza ɗaurin wata shida a gidan yari ko tarar naira 50,000 ba ko kuma a haɗa duka biyun.

A shekara ta 2007 ne aka ƙayyade kuɗin tarar, kuma ba a sake duba yawan kuɗin ba duk da tashin farashi da aka samu.

Duk da cewar dokar ta kwashe sama da shekara 17 amma ba a mayar da hankali kanta ba har sai cikin watannin da suka gabata, lokacin da hukumar EFCC ta fara dira kan masu cin mutuncin takardar naira.

Jami'ai sun ce watsa takardar kuɗin naira a lokacin shagulgula cin mutuncin ɗaya daga cikin manyan tambarin ƙasar ne.

Wasu kuma na cewa sabon shugaban hukumar ta EFCC da aka naɗa kwanan nan, Ola Olukoyede na neman suna ne kawai.

A cikin watan Fabarairu an ɗaure ƴar wasan fim Oluwadarasimi Omoseyin tsawon wata shida bayan kama ta da laifin liƙi da taka takardar kuɗin naira.

A watan da ya gabata ne fitaccen mai sanya kayan mata, wanda aka fi sani da Bobrisky ya amsa laifin cin mutuncin naira, kuma yanzu haka yana gidan kurkuku sanadiyyar hukuncin da aka yanke masa.

An ga Bobrisky a cikin bidiyo yana watsa kuɗi a lokacin bukukuwa da dama.

Photograph of Bobrisky after arrest

Asalin hoton, EFCC

Bayanan hoto, A watan Afrilu aka kama Bobrisky, kan zargin cin mutuncin takardar kuɗi ta naira

Bayan lokaci kaɗan kuma sai aka gurfanar da fitaccen ɗan kasuwa Cubana Chief Priest a kotu bisa zargin cin mutuncin takardar kuɗin naira.

Ya buƙaci a warware taƙaddamar a wajen kotu.

Hukumar EFCC ta ce akwai mutum 200 a faɗin Najeriya da ke fuskantar tuhuma kan cin mutuncin naira yayin da aka kama mutum 24 da laifi.

Sakamakon haka ne al'umma ke ci gaba da kai wa EFCC koke-koken mutane masu liƙi ko watsa kuɗaɗe a lokacin bukukuwa, sai dai hukumar ba za ta iya bin sawun dukkanin waɗanda ake kai ƙarar su wurinta ba.

Abu ne mai wahala a ce nan da nan za a iya kawar da wata ɗabi'a da ta zame wa al'umma jiki.

Wani masanin tarihi, Farfesa Tijjani Naniya ya ce al'ummar Najeriya ta fara rungumar ɗabi'ar bayar da kuɗi lokacin buki ne tun a shekarun 1940, lokacin da mutane ke kallon hakan a matsayin tallafa wa sabbin ma'aurata.

Ya shaida wa BBC cewa "Da farko mutane ba watsa kuɗi suke yi ba amma sukan riƙa sanya kuɗi ne cikin aljihun ango yayin da yake zaune".

"Wannan ce hanyar da suke taimaka masa...kasancewar zai fara hidimomi sosai da ke buƙatar kuɗi.

"Daga baya ne aka koma watsa kuɗi yayin da amarya da ango ke taka rawa. A wannan yanayin mai liƙa kuɗi na ƙoƙarin nuna cewa shi mai dukiya ne, kuma mutane suka riƙa yin gasa domin nuna cewa su ne suka fi watsa kuɗi a lokacin buki."

Farfesan ya ce zai yi wahala ƴan Najeriya su watsar da ɗabi'ar watsa kuɗi nan take, sai dai ya ce a yanzu abin ya ragu sanadiyyar matsi na tattalin arziƙi.

Sai dai abin a yanzu ba kawai a lokacin bukin aure ne ake yi ba.

...

Asalin hoton, Getty Images

Hadiza Usman, wadda cikin kwanakin nan aka yi mata liƙin kuɗi lokacin murnar zagayowar ranar haihuwarta ta ce ba ta tunanin cewa za a iya yin buki a Najeriya ba tare da liƙa kuɗi ba.

Ta ce "Mun taso mun ga iyayenmu na liƙa kuɗi a lokacin bukukuwa kuma hakan ya zamo tamkar al'adarmu."

A ɓangare ɗaya kuma akwai wasu mutanen kamar Usman Idris, waɗanda ba su taɓa liƙa kuɗi a lokacin buki ba kuma ba su sha'awar hakan.

Ya ce "Ba na ƙaunar ɗabi'ar - kasancewar tana nuna cewa kamar muna da arziƙi a ƙasar nan, bayan kuma ba haka ba ne, akwai talakawa da yawa.

"Malaman Musulunci sun daɗe suna wa'azi a kan hakan kuma a yanzu Musulmai kaɗan ne ke ci gaba da watsa kuɗi a yanzu."

Wasu malaman addini sun bayyana liƙa kuɗi a matsayin almubazzaranci, inda suka ce gara ma mutum ya bayar sadaka.

A wani yunƙurin hana mutane irin wannan ɗabi'a, wasu na cewa duk kuɗin da ka liƙa a wajen buki za su zamo wa mutum maciji a cikin kabari.

Wani mai sharhi kan lamurran yau da kullum, Sani Bala ya ce yana ganin wannan kame da ɗaure masu liƙin kuɗi ba zai haifar da sakamakon da ake sa rai ba.

Yanzu haka dai ba za a iya cewa matakin da hukumomi ke ɗauka ya yi tasirin a zo a gani ba.

A wasu bukukuwan masu liƙin kuɗi na hana a ɗauki hoto ko bidiyonsu, wasu kuma sun gwammace su dunƙula kuɗin su bai wa ma'aurata.

Su kuma shahararrun masu dukiya suna da wani zaɓin - ci gaba da watsa kuɗaɗen ƙasar waje, kamar dala da fam, kasancewar dokar ta shafi takardar naira ce kawai.