Atletico na zawarcin Alvarez wanda ke jan hankalin Arsenal, Newcastle na son Marc Guehi

Asalin hoton, Getty Images
Atletico Madrid na tattaunawa da Manchester City domin daukar dan wasan gabanta da kuma Argentina Julian Alvarez, mai shekara 24. (Athletic - subscription ), external.
Ita ma Arsenal na zawarcin Alvarez wanda ya lashe gasar cin kofin duniya, amma ana ganin sai Gunners ta kara sayar da wasu ‘yan wasanta domin ta iya samun kuɗin sayan sa. (Mirror), external
Newcastle na fatan samun nasara wajen sayan dan wasan bayan Ingila da Crystal Palace Marc Guehi, mai shekara 24. (Mail), external.
Palace ta fada wa Newcastle cewa ta na son kudi a kalla fam miliyan 50 da kuma Karin kudi domin ta sayar da Guehi. (Football Insider), external
Bournemouth ta dage cewa sai Tottenham ta biya fam miliyan 65 idan ta na son ta sayi dan wasan gaban Ingila Dominic Solanke, mai shekara 26,a wannan bazarar. (Mirror), external
Kungiyar ta kuma tuntubi Aston Villa da dan wasan gaban Ingila a tawagar masu shekaru 21 Cameron Archer, mai shekara 22, a matsayin wanda zai maye gurbin Solanke . (Teamtalk), external
RB Leipzig ta gargadi Barcelona cewa sai ta inganta sharudda kan dan wasan tsakiyar Sfaniya Dani Olmo, mai shekara 26, don kulla yarjejeniya kan yuro miliyan 61(90 min), external
Juventus na dab da sayan dan wasan bayan Nice da Faransa Jean-Clair Todibo, mai shekara 24, wanda a baya aka alakanta shi da Manchester United da West Ham. (La Gazzetta dello Sport - in Italian), external
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Juventus za ta koma Atalanta da kudi kusan yuro miliyan 55 domin sayan dan wasan tsakiyar Netherlands Teun Koopmeiners, mai shekara 26. (Corriere dello Sport - in Italian), external
Arsenal ta bukaci fam miliyan 30 tare da samun matsaya a kan duk wani alamarin da ya shafi sayarda dan wasan tawagar Ingila Eddie Nketiah, mai shekara 25, yayin da Marseille ke zawarcin dan wasan gaban. (Fabrizio Romano), external
Liverpool ta kosa ta kamala kula yarjejeniya da Lanus domin sayan dan wasan bayan Argentina Julio Soler a kan fam miliyan 13 wanda ta ke ganin zai iya maye gurbin dan wasan bayan Scotland Andrew Robertson, mai shekara 30. (Sun), external
Jean-Philippe Mateta, mai shekara 27, na son ya rattaba hannu kan sabon kwantiragi da Crystal Palace duk da cewa RB Leipzig da Napoli duk suna sha’awar dan wasan gaban Faransa . (Sun), external
Southampton na fatan Kyle Walker-Peters, mai shekara 27, zai ci gaba da taka leda a kungiyar a wannan bazara bayan West Ham ta janye daga tattaunawar da suke yi da shi domin daukarsa . (Football Insider), external
Watakila tsohon dan wasan bayan Aberdeen Scott McKenna ya koma kungiyar Las Palmas ta La Liga. Nottingham Forest ta salami dan wasan tsakiyar baya mai shekara 27 a wannan bazara .(Sun, external)
Liverpool na neman kudi a kalla fam miliyan 12 domin ta sayar da dan wasan tsakiyarta Bobby Clark, mai shekara 19, wanda Red Bull Salzburg, da Norwich da kuma Leeds ke zawarcinsa . (Athletic - subscription required), external











