Couto ya kammala komawa Dortmund daga Man City

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan Manchester City dan kasar Brazil, Yan Couto ya kammala komawa Borussia Dortmund.
An kulla yarjejeniyar da wadda ta buga wasan karshe a gasar zakarun Turai da cewar zai buga wasannin aro, daga baya ta saye shi kan £25.3m idan ya taka rawar gani.
"A gare ni mafarki na ne ya cika," in ji dan wasan mai shekaru 22, wanda ya koma City a shekarar 2020, wanda ya buga wasa a kungiyar da ke rike da Premier League.
"Borussia Dortmund kungiya ce ta musamman, kowane yaro a Brazil ya san fitatciyar kungiya ce.''
Bayan da ya koma City daga nan aka bayar da aronsa ga Girona na tsawon shekara guda, sannan ya je ya yi kaka biyu a Braga ta Portugal.
Ya taimaka wa Girona mai buga La Liga ta samu gurbin shiga gasar cin kofin zakarun Turai ta bana.







