Tinubu zai ƙaddamar da manufofinsa na shugabancin Najeriya

Bola Ahmed Tinubu

Asalin hoton, BABAJIDE SANWO-OLU/TWITTER

An wallafa

A yau Juma'a ne ɗan takarar shugabancin Najeriya na jam'iyyar All Progressive Congress (APC) zai bayyana wa al'umma manufofin da yake son aiwatarwa idan aka zaɓe shi muƙamin shugaban ƙasa a zaɓen 2023.

A cikin wata sanarwa ta hannun Bayo Onanuga, daraktan yaɗa labaru na kwamitin yaƙin neman zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasar na APC, ya bayyana cewar yau Alhamis ne za a gabatar da manufofin a wani gangami da za a yi a fadar shugaban Najeriya da ke Abuja.

Shugaba Muhammadu Buhari ne zai jagoranci taron, wanda kuma a lokacin ne ake sa ran ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen na Bola Ahmed Tinubu.

Jam'iyyar APC din dai ta sha ɗage lokacin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasar nata, bayan rashin jituwa da aka samu game da mutanen da kwamitin ya ƙunsa.

Bayanin sanarwar ya ce kundin manufofin Mr Tinubu mai shafuka 80, zai mayar da hankali ne a kan samar da tsaro, da bunƙasa tattalin arziƙi, da ɓangaren noma, da makamashi da sauran su.